Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

UNDP Ta Yaba Wa Gwamnatin Kaduna Bisa Shirye-Shiryenta Na Sana’o’i Da Ƙarfafa Tattalin Arziki

Shirin Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ya yabawa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa tsare-tsaren ta na zuba jari a ilimi mai dogaro ...

Shirin Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP) ya yabawa Gwamnatin Jihar Kaduna bisa tsare-tsaren ta na zuba jari a ilimi mai dogaro da sana’o’i, bunƙasa matasa, noma da kuma shirye-shiryen tallafin zamantakewa.

UNDP ta kuma  bayyana jihar  Kaduna matsayin abin koyi wajen gina jarin ɗan Adam da samar da ci gaba.

Wannan yabo ya fito ne a yayin wata ziyarar girmamawa da tawagar UNDP ƙarƙashin jagorancin Wakiliyar UNDP a Nijeriya, Misis Elsie Attahfua, ta kai wa Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, tare da jami’ai daga Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa.

A yayin ziyarar, ɓangarorin sun tattauna hanyoyin ƙarfafa haɗin gwiwa ta hanyar Shirin  wani shiri na Gwamnatin Tarayya da ake aiwatarwa ƙarƙashin Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, tare da goyon bayan UNDP da Tarayyar Turai, domin haɗa ilimi da bukatun kasuwacin

Tawagar UNDP ta jinjina wa Gwamnatin Kaduna bisa mayar da hankali kan koyar da sana’o’i da ƙarfafa matasa, tana mai bayyana kafa Cibiyar Koyar da Sana’o’i da Horaswa ta Jihar Kaduna a matsayin wata babbar shaida ta jajircewar gwamnati wajen samar da ilimi da ke shirya matasa kai tsaye zuwa aikin yi.

 Haka kuma, UNDP ta yabawa jarin da jihar ke zubawa a fannin noma da shirye-shiryen tallafin zamantakewa da ke inganta rayuwar jama’a da ƙarfafa tattalin arziki.

A jawabinsa, Gwamna Uba Sani ya yabawa UNDP bisa ci gaba da goyon bayan da take bai wa Jihar Kaduna a muhimman fannoni, yana mai cewa wannan haɗin gwiwa ya dace da manufar gwamnatinsa ta gina Kaduna mai haɗin kai, zamani da wayayyiya.

Gwamnan  ya kuma bayyana Shirin NJFP a matsayin wata muhimmiyar gada tsakanin ilimi da aikin yi, wadda ke bai wa matasa masu digiri damar samun ƙwarewar da ta dace da bukatun kasuwar aiki ta zamani.

Gwamnan ya jaddada cewa gwamnatinsa ta ɗauki zuba jari a kan mutane a matsayin ginshiƙi na ci gaba, yana mai cewa ilimi ba ya cika idan ba a haɗa shi da samar da ayyukan yi masu nagarta ba. Ya kuma tabbatar da aniyar Jihar Kaduna na ƙarfafa haɗin gwiwa da Gwamnatin Tarayya, UNDP da sauran abokan hulɗar ci gaba, musamman a muhimman fannoni kamar makamashi mai sabuntawa, noma, gine-gine da ayyukan hidima.

A ƙarshe, Gwamna Uba Sani ya tabbatar wa tawagar UNDP cewa Jihar Kaduna a buɗe take kuma a shirye take ga duk wata haɗin gwiwa da za ta dace da muradun ci gaban ta, yana mai nuna ƙwarin gwiwar cewa ci gaba da haɗin kai tsakanin gwamnati da abokan hulɗar ci gaba zai samar da Kaduna mai juriya, haɗin kai da wadata, wadda ke tafiya bisa jagorancin mutane masu ƙwarewa da hanyoyin ci gaba na cikin gida.

 

No comments