Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Tinubu Ya Yi Tuntube Ya Faɗi Yayin Liyafar Karbar Baƙi A Ƙasar Turkiyya

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗan yi tuntube na ɗan lokaci a ranar Laraba yayin wani bikin liyafar karbar baƙi da hukumomin ƙasar Turki...




Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya ɗan yi tuntube na ɗan lokaci a ranar Laraba yayin wani bikin liyafar karbar baƙi da hukumomin ƙasar Turkiyya suka shirya masa a wani bangare na ziyararsa ta aiki a ƙasar.

Lamarin ya faru ne a lokacin da Shugaba Tinubu ke tafiya a cikin jerin girmamawa na soji da aka tanada domin karbarsa a hukumance.

Wani bidiyo da ya yaɗu a kafafen sada zumunta ya nuna yadda shugaban ya ɗan kauce kaɗan daga takunsa, kafin ya daidaita kansa tare da ci gaba da tafiya ba tare da wata matsala ba.

Ba a samu wani tsaiko a cikin shirye-shiryen bikin ba, kuma shugaban ya ci gaba da dukkan sauran ayyukan da aka tsara masa a ziyarar. 

Jami’an Nijeriya da ke tare da shi ba su bayar da rahoton wata matsalar lafiya ko rauni da ya samu sakamakon lamarin ba.

Har zuwa lokacin haɗa wannan rahoto, fadar shugaban ƙasa ba ta fitar da wata sanarwa a hukumance dangane da batun ba. Sai dai hotunan bidiyon sun nuna cewa shugaban ya ci gaba da gudanar da ayyukansa cikin natsuwa da kwanciyar hankali.

Ziyarar da Shugaba Tinubu ke yi a Turkiyya na daga cikin kokarin gwamnatin Nijeriya na karfafa dangantakar diplomasiyya da kasashen waje, musamman a fannonin kasuwanci, zuba jari, tsaro da kuma raya ababen more rayuwa.

Nijeriya da Turkiyya sun daɗe suna da kyakkyawar alakar diplomasiyya, wadda ta kara ƙarfi a ‘yan shekarun nan ta fuskar hadin gwiwa a bangarori daban-daban. Tun bayan hawansa mulki a watan Mayun 2023, Shugaba Tinubu ya gudanar da ziyarce-ziyarcen qasashen waje da dama domin jawo masu zuba jari, fadada hulxar tattalin arziki da kuma karfafa matsayin Nijeriya a idon duniya.

Gwamnatinsa na mai da hankali kan gyaran tattalin arziki, karfafa zuba jari daga qasashen waje da kuma hadin gwiwar kasa da kasa a wani bangare na kokarin farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar.

Irin wannan dan tuntuve da shugabannin duniya ke yi a lokutan bukukuwa na hukuma ba sabon abu ba ne a idon jama’a, kuma a lokuta da dama ba ya shafar muhimman shirye-shiryen diplomasiyya.

No comments