Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya jaddada buƙatar gwamnati ta a riƙa yin saƙo iri ɗaya, daidaitacce, kuma wan...
Ministan ya yi wannan kiran ne a ranar Alhamis yayin wani taron tattaunawa da Daraktocin Yaɗa Labarai da kuma Jami’an Yaɗa Labarai (RIOs) da ke kan matakin aiki na 14 zuwa 17 waɗanda ma'aikatar sa ta tura Ma’aikatu, Sassa da Hukumomin Gwamnati (MDAs).
Taron, wanda aka gudanar a Abuja, yana da taken: “Daidaita Bayanan Gwamnati da Shirin Sabunta Fata: Sake Gina Amincewa ta Hanyar Ingantacciyar Sadarwa ta Gaskiya da Bayyana Komai.”
Idris ya ce samun amincewar jama’a shi ne mafi muhimmancin jari a harkar sadarwar gwamnati, yana mai jaddada cewa dole ne jami’an yaɗa labarai su kasance masu tsare gaskiya da amana da kuma daidaito wajen gudanar da ayyukan su.
Ya ce: “Samun yardar jama’a shi ne mafi muhimmancin jarin mu. Da zarar an rasa yardar jama'a, to babu irin saƙon da za a yi wanda zai gyara shi.”
Ya yi gargaɗin cewa rarrabuwar saƙwanni da hanyoyin sadarwa daban-daban yana rage amince wa gwamnati sannan yana jefa jama'ar ƙasa cikin ruɗani, inda ya jaddada cewa dole ne Gwamnatin Tarayya ta riƙa yin magana da murya guda, bayyananniya kuma mai daidaito.
“Mu gwamnati guda ɗaya ce wadda ke yi wa muradin ƙasa ɗaya hidima, don haka dole ne saƙon mu ya nuna wannan haɗin kan,” inji shi.
Ministan ya buƙaci Jami’an Yaɗa Labarai da su ɗauki kan su a matsayin cikakkun abokan aiki a inda aka tura su aiki, ba wai 'yan kallo kawai ba.
Ya ƙarfafa masu gwiwa da su riƙa hulɗa kai-tsaye da Ministoci, Manyan Sakatarori, da shugabannin hukumomi, yana mai cewa ƙwarewa da ƙwazo su ne ginshiƙan samun amincewa da tasiri.
Da yake magana kan ƙalubalen yaɗa labaran ƙarya da kuma saurin da kafofin sadarwa na zamani suke da shi, Idris ya jaddada muhimmancin isar da sahihin bayani cikin gaggawa, yana mai cewa jinkiri yakan bai wa labaran ƙarya damar su bazu.
Ko da yake ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na kare ’yancin faɗar albarkacin baki, ya ce dole ne a yi amfani da wannan ’yanci ta hanyar da ta dace.
Ministan ya kuma bayyana matakan da ake ɗauka domin ƙarfafa ƙwarewa a tsakanin jami’an yaɗa labarai, ciki har da wajibcin bayar da rahotannin aiki a kai a kai, inganta tsarin tura ma’aikata, horaswa mai ɗorewa da ƙarin tallafin hukumomi.
Ya bayyana cewa gwamnatin ta fara farfaɗo da Makarantar Horar da Jami’an Sadarwa ta Ƙasa (NIPI) domin haɓaka ƙwarewar jami’an yaɗa labarai na gwamnati.
A ƙarshe, Ministan ya yi kira da a ƙarfafa haɗin kai da mutunta juna, yana mai tunatar da mahalarta taron cewa su ne ginshiƙai wajen bayyana manufofi da nasarorin gwamnati, kuma dole ne su daidaita aikin su da muradun Shirin Sabunta Fata.
Taron ya samu halartar Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Harkokin Yaɗa Labarai da Ayyuka na Musamman, Mista Tunde Rahman; Babban Sakataren Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mista Ogbodo Chinansa Nnam; Darakta Janar na Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN), Malam Ali Muhammad Ali, wanda Babban Edita, Mista Mufutau Ojo, ya wakilta; Darakta Janar na gidan rediyon Muryar Nijeriya (VON), Malam Jibrin Baba Ndace; da Darakta Janar na Hukumar Gidajen Talbijin ta Ƙasa (NTA), Malam Salihu Dembos, tare da sauran manyan baƙi.









No comments