Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na gudanar da ƙidayar jama’a ta ƙasa...
Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya sake jaddada ƙudirin Gwamnatin Tarayya na gudanar da ƙidayar jama’a ta ƙasa wadda za ta kasance mai sahihanci, gaskiya kuma mai karɓaɓɓiya a idon duniya, inda ya bayyana cewa ingantacciyar sadarwa da haɗin gwiwar hukumomi su ne ginshiƙan samun nasarar aikin.
Ministan ya bayyana hakan ne a Abuja a jiya, lokacin da ya karɓi Shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf, wanda ya jagoranci tawagar shugabannin hukumar a wata ziyarar girmamawa da suka kai masa.
A cewar Idris, sahihan bayanai su ne tushen tsare-tsaren ƙasa, yana mai jaddada cewa ba tare da cikakkun bayanan yawan jama’a ba, ba za a iya tsara cigaba mai ma’ana da kuma tasiri ba.
Ya tabbatar wa da shugabannin NPC cewa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da hukumomin ta—ciki har da Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), Gidan Talbijin na Ƙasa (NTA), Hukumar Rediyon Tarayya ta Nijeriya (FRCN), Muryar Nijeriya (VON) da Hukumar Dillancin Labarai ta Nijeriya (NAN)—a shirye suke tsaf wajen wayar da kan ’yan Nijeriya da kuma jagorantar yaɗa saƙonni a faɗin ƙasar nan da zarar Shugaban Ƙasa ya ayyana ranar ƙidayar.
Ministan ya jaddada cewa gwamnatin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu tana da niyyar gudanar da ƙidayar da ’yan Nijeriya da al’ummar duniya za su yarda da ingancin ta, yana mai cewa gwamnatin na bai wa tsari, bin doka da sahihanci fifiko fiye da yin gaggawa.
Ya sake nanata cewa ayyanawar Shugaban Ƙasa ita ce tushen doka ta gudanar da ƙidayar jama’a, yana mai tabbatar da cewa Shugaba Tinubu yana daidaita dukkan abubuwan da ake buƙata yadda ya kamata domin aikin ya cika ƙa’idojin duniya.
Ministan ya yi kira ga NPC da ta ci gaba da amfani da kafafen yaɗa labarai na gwamnati wajen wayar da kan jama’a, yayin da ya ba da tabbacin cewa ma’aikatar sa za ta sauke nauyin da ke kan ta na tallata shirye-shirye da manufofin gwamnati bisa muradin ƙasa.
Tun da fari, sai da Shugaban Hukumar Ƙidayar Jama’a ta Ƙasa (NPC), Dakta Aminu Yusuf, ya yaba wa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai bisa goyon baya da jagoranci da take bayarwa a ƙoƙarin wayar da kan jama’a gabanin ƙidayar da aka ɗage.
Ya ce hukumar tana cikin shirin ko-ta-kwana, inda ake ci gaba da inganta tsare-tsare, kayan aiki, fasahar sadarwa (ICT) da ma’aikata domin tabbatar da inganci, gaskiya da sahihanci da zarar an bayyana sabuwar ranar ƙidayar.
Dakta Yusuf ya kuma buƙaci a ci gaba da ba su damar yin amfani da kafofin yaɗa labarai na gwamnati domin zurfafa fahimtar jama’a kan muhimmancin shiga ƙidayar, rajistar haihuwa da mutuwa, da muhimman ƙididdiga, yana mai bayyana cewa amincewar jama’a ita ce jigon nasarar tafiyar da al'amurran ƙididdiga a Nijeriya.




No comments