Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

HARIN KURMIN WALI: Waɗanda Abin Ya Rutsa Da Su Sun Faɗi Yadda Suka Ji

Kwanaki huɗu bayan kai hari a garin Kurmin Wali da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna, wasu da harin ya rutsa da su sun fara bayyana i...


Kwanaki huɗu bayan kai hari a garin Kurmin Wali da ke Ƙaramar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna, wasu da harin ya rutsa da su sun fara bayyana irin mawuyacin halin da suka tsinci kansu a ciki, tare da jaddada ƙwarin gwiwa ga jagorancin Gwamna Uba Sani.

Ɗaya daga cikin waɗanda suka tsira, Mista Joseph, ya ce maharan sun kai farmaki ne cikin al’ummar a safiyar Lahadi yayin da jama’a ke cikin ibada. Ya bayyana cewa maharan sun umurci masu ibadar da su kwanta rub-da ciki kafin su tilasta musu zuwa wani daji da ke kusa.

A wata zantawa da manema labarai, waɗanda suka tsiran Sun kuma jadadda ƙwarin gwiwarsu dangane da ƙoƙarin gwamnan jihar Kaduna Uba Sani.

A cewarsa, ya samu damar tserewa ne a lokacin da rikici ya barke, sannan daga bisani ya samu ya tsira ya isa wuri mai aminci.

Duk da mummunan abin da ya faru, Mista Joseph ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa yadda ya kai ziyara Kurmin Wali da kansa domin jajanta wa waɗanda abin ya shafa tare da tantance halin da ake ciki. Ya bayyana jagorancin gwamnan a matsayin na tausayi da kula da jin daɗin al’umma.

Ya ƙara da nuna kwarin gwiwa ga ƙudurin gwamnan wajen tabbatar da tsaro da walwalar mazauna jihar, tare da yi masa addu’ar samun nasara da ci gaba da jagoranci nagari.

A halin da ake ciki kuma, majiyoyi sun tabbatar da cewa an kwashe waɗanda harin ya rutsa da su zuwa Kaduna domin samun kulawar lafiya da tallafin shawarwari na kwakwalwa, bisa ga alƙawurran da Gwamna Uba Sani ya bayar a lokacin ziyarar.


 

No comments