Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

CBN Zai Fito Da Tsarin Magance Yawan Samun Matsalolin Katin ATM Da Na'urorin ATM

Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana shirin ƙaddamar da sabuwar dokar tsari da nufin daidaita fitar da katinan cire kuɗi da kuma ayyukan ...


Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bayyana shirin ƙaddamar da sabuwar dokar tsari da nufin daidaita fitar da katinan cire kuɗi da kuma ayyukan na’urorin ATM a bankunan Nijeriya, domin magance matsalolin cinkoso da wahalar samun kuɗi.

Gwamnan CBN, Yemi Cardoso, ya bayyana hakan ta hannun mai ba shi shawara na musamman, Fatai Karim, a wajen Taron Kwamitin Shugabannin Ayyukan Bankuna na shekarar 2026 da aka gudanar ranar Juma’a.

A cewar babban bankin, sabuwar dokar za ta tabbatar da cewa adadin katunan da bankuna ke fitarwa ya dace da yawan na’urorin ATM da suka girke, domin rage cinkoso, yawan lalacewar ATM, da rashin daidaiton samun kuɗi a faɗin ƙasar.

CBN ta bayyana cewa matsalolin lalacewar ATM akai-akai da ƙarancin kuɗi suna ci gaba da rage ƙarfin amincewar jama’a ga hanyoyin biyan kuɗi na zamani, duk da cewa mu’amalar kuɗi ta hanyar zamani na ƙaruwa cikin sauri a ɓangaren bankuna.

“Ba da daɗewa ba, Babban Bankin Nijeriya zai fito da wata sabuwar doka domin gyara da inganta wannan yanayi, musamman game da adadin katunan da bankuna ke fitarwa idan aka kwatanta da yawan ATM da suke tallafawa. Idan samun kuɗi ya gaza, ko saboda samun cikas da tangarɗar lalacewar ATM ko rashin daidaiton rarraba kuɗi, hakan na raunana amincewar tsarin biyan kuɗi gaba ɗaya,” inji bankin.

Karim ya ƙara da cewa, "CBN na tattaunawa da masu ruwa da tsaki a ɓangaren, kuma ana sa ran dokar za ta fara aiki cikin ‘yan watanni, mai yiyuwa kafin ƙarshen zango na biyu na shekarar 2026.
Ana sa ran wannan mataki zai inganta amincin ATM, ya daidaita rarraba kuɗi, tare da dawo da amincewar jama’a ga tsarin biyan kuɗi na zamani a Nijeriya, abin da zai amfani bankuna da kwastomomi a duk faɗin ƙasar."
 

No comments