Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana Dagacin Garin Yankin Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Alhaji Rabiu Isyaku da cewa jagora ne mai ƙwazo da kis...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana Dagacin Garin Yankin Ƙaramar Hukumar Nasarawa, Alhaji Rabiu Isyaku da cewa jagora ne mai ƙwazo da kishin ci gaban al'ummar da yake bayar da gagarumar gudumawa wajen tabbatar da haɗin kai da zaman lafiya da kyakkyawan tarbiyya a tsakanin al'ummar garin Gama .
Dogarin matar shugaban ƙasa, ACP Bello Yakubu ne ya bayyana hakan a yayin taron bukin cikar Dagacin Garin na Gama, Alhaji Rabiu Isyaku shekaru 25 da aka gudanar a ranar Lahadi.
ACP Bello Yakubu, wanda ɗan uwan sa, Alhaji Aminu Yakubu ya wakilta a taron, ya ce suna yi wa mai Garin Gama fatan alhairi bisa irin kyawawan shugabancin wannan masarauta ta Gama da ya ke, tare da yi masa addu'ar Allah ya ƙara masa ƙwarin gwiwa wajen ci gaba da tafiyar da masarautar da ya kawo wa al'ummar ta ƙarin ci gaba.
Ya yi nuni da cewa magana ta gaskiya, duk wanda ya san garin Gama shekaru 25 da suka wuce ya san irin ƙalubale na tsaro da ta ke ciki na yawan faɗan daba da ake samu da masu ta'ammali da shan miyagun ƙwayoyi.
ACP. Bello Yakubu ya ce naɗa Dagacin a lokacin yana matashi ya haɗa kan al'umma, ya yi ƙoƙarin hana daba da Shaye-shaye tun daga lokacin da Gama ta samu take zauna lafiya da wuya ka ga ana harkar daba ko wani abu da bai dace ba, ya kawo ci gaba sosai da zaman Lafiya.
Daga nan ACP Bello Yakubu ya yi kira ga al'ummar Gama su ci gaba da bai wa Dagaci Alhaji Rabiu Isyaku goyon baya da gudumawa, tare da yi masa addu'o'in fatan alhairi akan irin ayyukan da ya ke yi.

No comments