Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Yadda Majalisar Dattawa Ta Yi Muhawara Mai Zafi Kafin Amincewawa Da Sabon Ministan Tsaro

Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da naɗin tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, a matsayin Ministan Tsaro bayan shafe k...




Majalisar Dattawan Nijeriya ta tabbatar da naɗin tsohon Babban Hafsan Tsaro, Janar Christopher Musa, a matsayin Ministan Tsaro bayan shafe kusan sa’o’i biyar ana yi masa tambayoyi a zaman tantance shi da aka gudanar a ranar Laraba.

Rahotanni sun nuna cewa zaman ya shiga yanayi na ɗan ɗar-ɗar tun da fari, yayin da wasu sanatoci suka yi ƙoƙarin a bar Janar Musa ya gaishe da majalisar kawai ya wuce, kamar yadda ake yi wa wasu. Sanata Sani Musa na yankin Neja ta Gabas ne ya fara roƙon majalisar da a bar tsohon hafsan tsaron ya yi gaisuwa bayan ‘yan kaɗan daga tambayoyi.

Sai dai wannan roƙo ya gamu da adawa mai ƙarfi daga wasu sanatoci da suka dage cewa dole ne a yi masa cikakken tantancewa saboda muhimmancin ma’aikatar da zai jagoranta a daidai lokacin da ƙasar ke fama da matsalolin tsaro. Hakan ya janyo hayaniya a zauren majalisar, inda wasu sanatoci suka tsaya tsayin daka suna neman a zurfafa tambayoyi.

A ƙarshe, Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya tashi tsaye, wanda a dokar majalisa ke nuni da kiran zaman tsitsiya. Ya bukaci sanatoci su kwantar da hankali, tare da jaddada cewa manufar tantancewar ita ce tabbatar wa ‘yan Nijeriya cewa za su samu amintattun matakai na kare rayuka da dukiyoyi a wannan lokaci na ƙalubalen tsaro.

Akpabio ya kuma bukaci Janar Musa ya yi cikakken bincike kan rahoton da ke cewa an janye sojoji daga wata makaranta a Jihar Kebbi, inda daga baya aka yi garkuwa da ‘yan makaranta mata. Wannan batu ya zama ɗaya daga cikin muhimman tambayoyin da suka dauki hankalin sanatoci.

Da yake amsa tambayoyin, Janar Musa ya bayyana matuƙar damuwarsa kan tsananin rashin tsaro da ke addabar ƙasar, yana mai cewa lamarin abin takaici ne ƙwarai. Ya nanata buqatar ƙarfafa shirin kare makarantu, inda ya ce har yanzu makarantu da dama na cikin barazana.

Ya kuma jaddada muhimmancin gina ƙarfinsu al’ummomin ƙasa, tare da amfani da dabarar haɗin gwauron zabi wadda ke haɗa fasaha, sa hannun al’umma da kuma daidaitattun ayyukan jami’an tsaro. A cewarsa, wannan ne kadai zai iya kawo ƙarshen yawaitar sace-sacen mutane.

Tsohon hafsan tsaron ya kuma yi kira da a ƙara tsaftace harkokin aiki a cikin rundunonin tsaro, tare da buƙatar cikakken haɗin kai tsakanin ma’aikatun gwamnati, hukumomi da sassan tsaro. Ya ce yawancin hukumomi ba sa aiki da cikakken ƙarfinsu, kuma dole ne su daidaita rawar da kowa ke takawa, har ma da haɗin gwiwa da ƙasashen makwabta, ganin yadda ta’addanci ke da yanayin ƙetare iyaka.

Janar Musa ya gargaɗi cewa Nijeriya na da asara mai yawa idan hukumomin tsaro suka gaza yin aiki tare, yana mai cewa ‘yan ta’adda na kallon ƙasar a matsayin wadda ke da arziki, saboda haka suke kai mata hare-hare. Ya jaddada buƙatar tsauraran matakai na rashin sassauci kan ta’addanci da fashi, bisa haɗin gwauron zabi da al’ummomin gari.

Har ila yau, ya bayyana cewa wasu dokoki da ake amfani da su yanzu sun tsufa kuma suna buƙatar sabuntawa cikin gaggawa. Ya kuma bayyana cewa haƙar ma’adanai ba tare da ka’ida ba na daga cikin manyan hanyoyin samun kuɗin da ƙungiyoyin masu aikata laifuka ke amfani da su, yana mai kira da a tsaurara sa ido ta hanyar amfani da na’urorin zamani.

A ƙarshe, bayan kammala tantancewa da muhawara, Majalisar Dattawa ta kada ƙuri’a tare da amincewa da naxa Janar Christopher Musa a matsayin sabon Ministan Tsaron Nijeriya.

Haka kuma,  an tabbatar da shi ne ranar Laraba ta hanyar ƙuri’ar murya, bayan zaman tantancewa da ’yan majalisar suka gudanar a zauren su na Kwamitin da ya haɗa kowa da kowa, inda suka tambaye shi jerin tambayoyi masu yawa kan aikin tsaro da makomar rundunonin soji.

Janar Musa, wanda ya yi murabus daga aikin soja kusan kwanaki 40 da suka gabata, shi ne Shugaba Bola Tinubu ya sake gabatar wa majalisar a matsayin zabinsa na Ministan Tsaro a ranar Talata, tare da neman gaggawar tabbatar da shi.

A yayin zaman tantancewar, ’yan majalisar sun tattauna da shi kan batutuwan da suka shafi tsaro, matsalolin hare-hare da suke fuskantar ƙasar, da sabbin dabarun da ake sa ran zai kawo domin ƙarfafa tsaron ƙasa.

Majalisar ta amince da nadin nasa bayan ba a sami wata adawa kai tsaye ba a zauren majalisar.

No comments