Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaryata kalaman Shugaban ƙasar Amurka, Donald J. Trump, wanda ya yi iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci da yaw...
Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta ƙaryata kalaman Shugaban ƙasar Amurka, Donald J. Trump, wanda ya yi iƙirarin cewa ana kashe Kiristoci da yawa a Nijeriya, tare da kira da a sanya ƙasar cikin jerin ƙasashen da ke take haƙƙin addini.
A cikin wata sanarwa da Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar ranar Asabar, 1 ga Nuwamba, 2025, mai ɗauke da sa hannun Kimiebi Imomotimi Ebienfa, mai magana da yawun Ma’aikatar, gwamnatin ta ce kalaman Trump ba sa nuni ga ainihin halin da ake ciki a ƙasar ba.
Sanarwar ta ce: “Nijeriya tana godiya da damuwar ƙasashen duniya game da kare haƙƙin bil’adama da ‘yancin addini, amma wannan iƙirari ba shi da tushe. ‘Yan Nijeriya mabiya dukkan addinai suna rayuwa, aiki da kuma ibada tare cikin lumana.”
Ma’aikatar ta ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da jajircewa wajen yaƙi da ta’addanci, ƙarfafa zumuncin addinai, da kare rayuka da haƙƙoƙin dukkan ‘yan ƙasa.
Nijeriya ta kuma bayyana cewa za ta ci gaba da yin aiki tare da gwamnatin Amurka domin inganta fahimtar juna kan harkokin yankin da kuma ƙoƙarin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.

No comments