Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamna Uba Sani Ya Kashe Naira Biliyan 8.2 Kan Aikin Hanyar Kabala Costain – Daraktan KADRA

An bayyana cewa a ƙoƙrin sa na inganta rayuwar al'umma, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kashe jimillar kuɗi Naira Biliyan 8.2 ...


An bayyana cewa a ƙoƙrin sa na inganta rayuwar al'umma, Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kashe jimillar kuɗi Naira Biliyan 8.2 wajen biyan bashin da aka gada da kuma sake farfaɗo da aikin hanyar Kabala–Costain da ke cikin Ƙaramar Hukumar Kaduna ta Arewa wanda gwamnatin da ta gabata ta yi watsi da shi a baya.

Shugaban Hukumar kula da Hanyoyi ta Jihar Kaduna (KADRA), Dakta Abdullahi Baba Ahmed ne ya bayyana haka yayin da ya kai ziyara domin duba halin da aikin ke ciki.

Ya ce gwamnatin da ta gabata ta bar aikin ne saboda matsalolin tsari da kuma rashin isasshen kuɗin gudanarwa, wanda yanzu gwamnatin Uba Sani ke ci gaba da aiwatarwa.

Dakta Ahmed ya bayyana cewa Gwamna Uba Sani ya biya bashin Naira Biliyan 2.2 da 'yan kwangilar ke bi, sannan ya sake tura kamfanin CCECC zuwa wurin aikin da ƙarin Naira Biliyan 6.

Ya ƙara da cewa, zuwa yanzu an kashe jimillar kuɗi Naira Biliyan 8.2 kan aikin, kuma akwai tabbacin cewa za a kammala shi nan da shekara mai zuwa.

Shugaban na KADRA ya kuma ce gwamnatin Uba Sani ta gaji aikin hanyar Kabala–Costain ne a matakin kashi 35 cikin 100 kacal na kammalawa, sabanin ikirarin da gwamnatin da ta gabata ta yi.

Shi ma babban mai ba da shawara akan aikin  hanyar, Injiniya Shakirudeen Adesina Akinloye, ya bayyana cewa an kaddamar da kwangilar aikin ne tun a shekarar 2020, amma ya tsaya cak a 2022 saboda matsalolin tsari da kuma rashin biyan kuɗi, wanda ya tilasta kamfanin CCECC ya dakatar da aiki.

Injiniya Akinloye ya ce gwamnatin Uba Sani ba kawai ta sake farfado da aikin ba, har ma ta biya bashin Naira biliyan 2.2 da gwamnatin da ta gabata ta bari.

“Aikin ya tsaya a kashi 35 cikin 100 kafin gwamnati ta yanzu ta karɓe shi. Bayan dawowarmu, mun gano cewa tsarin farko yana da matsala ,  akwai lanƙwasa a ciki  gadar wanda zai iya haddasa haɗura. Mun sake tsara hanyar domin tabbatar da kwanciyar hankali da tsaron masu amfani da hanya,” in ji shi.

Dakta Baba Ahmed ya kara jaddada cewa gwamnati ta gaji aikin a kashi 35 cikin 100 kacal na kammalawa, inda ya ce ginin gada guda daya ne kacal da kuma kusan mita 600 na hanya daga cikin jimillar kilomita 2.7 aka gama, wanda ke wakiltar kusan kashi 22 cikin 100 na aikin gaba daya.

“Wannan gwamnati ta hau karagar mulki a 2023 ta kuma farfado da aikin. Ta biya bashin Naira biliyan 2.2 ga mai kwangilar sannan ta bayar da karin kashi 50 cikin 100 na kudin aikin da ya rage,” in ji shi.

Shugaban KADRA ya karyata ikirarin cewa gwamnatin da ta gabata ta kai aikin kashi 70 cikin 100, yana mai cewa hakan “ba gaskiya ba ne.”

“Wannan lissafi ne mai sauƙi. Mita 600 cikin kilomita 2.7 na nufin kashi 22 cikin 100. Wannan gwamnati ce ke gina sauran kilomita 2.1 da kuma gada ta biyu,” in ji shi.

Aikin faɗaɗa titin Kabala–Costain mai tsawon kilomita 2.7 yana haɗa titin Aliyu Makama da Costain Junction a Kaduna ta Arewa.

Da zarar an kammala shi, ana sa ran zai rage cunkoson ababen hawa, hana ambaliyar ruwa, tare da ƙarfafa alaƙar tattalin arziki tsakanin Kaduna ta Arewa da Kaduna ta Kudu.

Ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa jajircewarsa wajen tabbatar da cewa aikin an .kammala shi cikin nasara.

 

No comments