Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

An Caccaki Shugaban SUBEB Bisa Tilasta Wa Malamai Sharar Makaranta A Gaban Ɗalibai

Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ta caccaki Shugaban Hukumar Ilimi ta Firamare (SUBEB) na jihar, Farfesa Raheem Adaramaja, bisa zargin tilasta ma...


Jam’iyyar PDP a Jihar Kwara ta caccaki Shugaban Hukumar Ilimi ta Firamare (SUBEB) na jihar, Farfesa Raheem Adaramaja, bisa zargin tilasta malamai — har ma da mataimakin shugaban makaranta — su share filin makaranta a gaban ɗalibai yayin ziyarar da ya kai Makarantar Sakandaren Gwamnati da ke Amule.

Shaidu sun bayyana cewa Farfesa Adaramaja ya yi zargin cewa ba a tsaftace muhallin makarantar, inda ya buƙaci malamai su tattara shara, duk da cewa an shaida masa ɗalibai ne suka koma daga hutu a lokacin.

A wata sanarwa, mai magana da yawun PDP na jihar, Olusegun Olusola Adewara, ya bayyana abin da ya faru a matsayin wulaƙanci da cin mutunci ga malamai, yana mai cewa hakan ba aiwatar da doka ba ne, illa nuna ƙarfin mulki da take haƙƙin ma’aikata a idon ɗalibai.

PDP ta tambayi Gwamna Abdulrahman Abdulrazaq ko wannan ne sabon matsayin da gwamnatin jihar ta ɗauka kan darajar malamai, tana mai jaddada cewa aikata hakan daga farfesa da ya taɓa koyarwa ya nuna raini, girman kai da rashin tausayi.

Kungiyar Malamai ta NUT ta reshen Ilorin ta nuna goyon baya ga Malaman, inda shugaban reshen, Comrade Saka Saafi Adanla, ya bayyana abin da ya faru a matsayin abin kunya da ba za a lamunta ba, yana mai buƙatar cikakken bayani daga shugaban SUBEB.

Ya ƙara da cewa, ƙungiyar na aiki tuƙuru domin tabbatar da kare mutuncin malamai da tabbatar da irin wannan abu ba zai sake faruwa a jihar ba.

A halin yanzu, PDP ta buƙaci gwamnan ya ɗauki mataki kan shugaban SUBEB tare da yin tir da abin da ya faru, domin tabbatar da cewa mutuncin ma’aikata na ci gaba da kasancewa abin girmamawa a Kwara.
 

No comments