Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Ya Kwanta Dama

Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu bayan ya shafe dogon lokaci yana fama da jinya. Wani makusancin iyal...




Fitaccen malamin addinin Musulunci, Sheikh Dahiru Usman Bauchi, ya rasu bayan ya shafe dogon lokaci yana fama da jinya.

Wani makusancin iyalansa ya tabbatar da rasuwar ga manema labarai, ya bayyana mutuwar a matsayin babbar rashi ga al’ummar Musulmi da kuma Æ™asa baki É—aya.

Majiyar ta ce, rasuwarsa ta girgiza mabiyansa da É—alibansa a sassan Nijeriya da Æ™asashen waje, yana mai jaddada cewa marigayin ya shafe rayuwarsa yana hidimar ilimin addini, tarbiyya da kuma wa’azi na zaman lafiya da daidaito.

Har zuwa lokacin haÉ—a wannan rahoto, iyalansa ba su sanar da cikakken lokacin jana’iza ba, sai dai ana sa ran za su fitar da sanarwa nan ba da jimawa ba domin sanar da jama’a lokutan jana’iza da sauran al’amuran da suka dace.

Sheikh Dahiru Usman Bauchi na daga cikin manyan malaman da suka yi tasiri sosai a harkar da’awa da koyar da addinin Musulunci a Nijeriya tsawon shekaru da dama, inda dubban É—alibai suka ci gajiyar karatunsa da koyarwarsa. 

Mutuwarsa ta haifar da saÆ™onnin jaje daga bangarori daban-daban na al’umma.

No comments