Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SHAIKH MASUSSUKA: Gwamnatin Katsina Za Ta Gudanar Da Zama Na Musamman Don Kare Kai

Sakamakon koke-koken da Malam Izala ke yawan aikawa game da salon wa'azin Mahaddacin Alƙur'anin nan da ke Katsina, Shaikh Yahaya Mas...

Sakamakon koke-koken da Malam Izala ke yawan aikawa game da salon wa'azin Mahaddacin Alƙur'anin nan da ke Katsina, Shaikh Yahaya Masusska, gwamnatin jihar ta sanar da cewa za ta shirya wani zama na musamman domin kowa ya kare kan sa, inda a ƙarshe za a fitar da matsayar za a tilasta wa kowa sai ya bi.


A cikin wata sanarwar manema labarai da ta fito daga ofishin Sakataren gwamnatin jihar, wacce Daraktan yaÉ—a labarai na ofishin, Ibrahim Almu Gafai ya sanya wa hannu a yau Talatar nan, ta bayyana cewa tun farko gwamnatin ta tura maganar zuwa gaban mai martaba Sarkin Katsina Abdulmumin Kabir Usman, CFR domin a yi wa tukka hanci, amma sai abin bai yiwu ba.

A sanarwa, an bayyana cewa "gwamnatin jihar Katsina ta karbi koke-koke game da salon wa'azin Malam Yahaya Masussuka, wanda suka ce ya saba ma koyarwar addinin musulunci.

"Haka kuma gwamnatin ra karbi wani koken daga shi Malam Yahaya Masussuka, inda ya ke kokawa da cewa 'yan ƙungiyar Jama'atu Izalatul Bid'a suna zazzagin sa, tare da yi wa rayuwar sa baraza."

Gwamnatin ta ce, "wannan ne ya sa ta tura wannan magana zuwa masarautar Katsina, Æ™arÆ™ashin jagorancin Alhaji Abdulmumin Kabir Usman, CFR. 

"Sarkin ya kira duk bangarorin biyu, inda aka tattauna, wanda kuma Sarkin ya hore su da cewa kar wanda ya yi wa'azin da zai cutata wa É—an uwan sa musulmi."

Gwamnatin ta ce, amma bayan wannan zaman, ta samu labarin cewa wannan hayaniyar ta ci gaba. "Don haka, saboda da a samu zaman lafiya da fahimtar juna, Gwamnan jihar, Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bayar da umurnin cewa a sanar da Malam Yahaya Masusska ya shirya kare kan sa bisa zarge-zargen da ake yi masa, zai gurfana gaban wani kwamiti na Malamai, inda za a fitar da tsare-tsre da ƙa'idojin da kowa dole ya bi.

"Za a zauna a fitar da tsayayyun ƙa'idoji, wanda kuma duk wanda ya saba da su, to gwamnati za ta ɗauki tsattsauran mataki a kan sa," inji sanarwar.


 

No comments