Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Magoya Bayan Wamban Shinkafi Sun Goyi Bayan Tinubu Shugaban Ƙasa A Karo Na Biyu

Daga Hussaini Yero  Masu ruwa da tsaki na tafiyar Wamban Shinkafi, Sani Abdullahi, ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar APC a jihar Zamfara sun am...



Daga Hussaini Yero 

Masu ruwa da tsaki na tafiyar Wamban Shinkafi, Sani Abdullahi, ƙarƙashin inuwar Jam'iyyar APC a jihar Zamfara sun amince da Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar a zaɓen 2027.

Da yake jawabi a taron masu ruwa da tsaki na jam'iyyar a Taula Arena da ke Gusau yau Talata, Shugaban ƙungiyar, Hon. Yusha'u Abdullahi Mada wanda ya gabatar da buƙatar sake zaɓen Shugaba Tinubu kuma Asma'u Bello Gusau ta goyi bayan sa, ya ce Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya cancanci sake zaɓensa a matsayin Shugaban ƙasa a 2027.

Mada ya bayyana cewa, Shugaba Tinubu ya yi abubuwa da yawa na amfanar talaka da kuma shawo kan tattalin arzikin ƙasar daga rugujewa.

 Da yake jawabi a lokacin taron, jigo a a tafiyar ,Sani Abdullahi Shinkafi, ya yi kira ga dukkan magoya bayansa da kuma na jam'iyyar APC a Kananan hukumomi goma sha huɗu na jihar Zamfara da su nuna goyon bayansu ga jam'iyyar APC da kuma dan takarar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027".

"Muna tare a tafiya A APC A Zamfara karkashin Sanata Abdulaziz Yari Abubakar saboda jajircewarsa wajen ci gaban jihar Zamfara, yankin Arewa maso Yamma da kuma bayan haka, wanda hakan ya nuna cewa ya amfana da dimbin rabon dimokuradiyya da Tinubu ke bayarwa.

"Ina goyon bayan dukkan manufofin da Sanata Abdulaziz Yari Abubakar ya yi, yayin da ya bayyana kwanan nan cewa ba za a tilasta wa dukkan 'yan takara a APC a jihar ba, saboda haka, ina sanar da ku cewa burina na zama dan Takarar gwamna yana nan daram kamar yadda na dade ina fafutukar yi tsawon shekaru."

 "Dole ne a gudanar da zaɓen farko a APC nan da shekarar 2027 kawai don tabbatar da zaman lafiya da haɗin kai tsakanin magoya baya, wanda hakan zai iya dawo da martabar APC da ta ɓace a Jihar Zamfara, don haka, ina yi kira ga dukkan 'yan jam'iyyar da ke da sha'awar tsayawa takara a kowace kujera ta siyasa da su bayyana burinsu cikin sauri," in ji Shinkafi.

Ya kuma yi kira da a goyi bayan Shugaba Bola Tinubu don a sake zaɓensa nan da shekarar 2027 domin rage farashin abinci, samun saukin matsalar rashin tsaro ya ci gaba da raguwa gwargwadon yadda manoma za su koma gonakinsu kuma talauci da rashin aikin yi a tsakanin matasa za kare da yardar Allah.
 

No comments