Daga Zubairu Lawal, Lafia Kamfanin sarrafa shinkafa na NASACCO RICE, wanda aka samo daga Nasarawa Agro Commodity Company ya samu haɗin giwa...
Daga Zubairu Lawal, Lafia
Kamfanin sarrafa shinkafa na NASACCO RICE, wanda aka samo daga Nasarawa Agro Commodity Company ya samu haɗin giwa da Silvex International domin bunƙasa tattalin arzikin jihar da samar da wadacecen abinci a Nigeria.
Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa ne ya bayyana haka a ranar Litinin a garin Jangwa da ke Ƙaramar Hukumar Obi ta jihar yayin bikin fara girbin gonar shinkafar da ke Garin Jangwa a yankin Agwatashi cikin jihar.
Gwamnan ya bayyana cewa kamfanin Silvex International ta amince da sunan Nasacco Rice wanda za a sarrafa a sanya cikin buhu mai inganci.
Gwamna Sule ya ce shiga jihar Nasarawa cikin harkar noman shinkafa wani babban ci gaba ne, domin Noma shi ne tushin arzikin kowace ƙasa da ta ci gaba a duniya.
Gwamnan ya ce kamfanin Sives International kamfanin da ke da ingantatun injunan sarafa shinkafa, ɗaya a Kogi, ɗaya a Abuja, amma ba su da gonaki. Suna sayen shinkafa daga kasuwa. Amma yanzu, maimakon su sayo daga kasuwa, mun nemi su sayo daga gare mu.
Ya ce; Gwamnatin jihar tana taimaka wa manoman ta da kayan aikin noma, kamar Motochin noma, takin zamani, maganin ciyawa da sauransu.
Gwamnan ya nuna matuƙar farin ciki da yadda girbin shinkafar ya kasance, yana mai cewa amfanin da ake samu daga kowace Hekta yana da kyau.
Ya ce; “A bara muna da gonar shinkafa ta Eka 2,000, muka gwada, amma a bana mun ƙara Eka 1,300, jimillar su ta kai eka 3,300. Insha Allah, a kakar gaba za mu ƙara eka 2,000, don mu kai fiye da eka 5,000,” in ji shi.
Shi ma mai kula da harkokin kamfanin Silvex International, Mista Abubakar Garba Ibrahim, ya yaba wa Gwamna Sule bisa jajircewar sa wajen sauya tsarin harkar noma.
Ya bayyana cewa ingancin shinkafar Jangwa yana da kyau ƙwarai, yana mai cewa irin shinkafar da aka noma a jihar tana daga cikin mafi kyau.
“Silvex kamfani ne da ke gudanar da harkar noma daga tushe har zuwa sarrafawa, kuma muna da ƙarfin sarrafa shinkafa tan 460 a rana – wanda ya kai motoci fiye da 15 – daga masana’antunmu biyu da ke kusa da jihar Nasarawa.
"Amma babban ƙalubale gare mu shi ne samun shinkafa mai inganci a farashin da zai dace domin mu iya sarrafa ta don kasuwar Najeriya. Abin farin ciki, yanzu mun samu abokin hulɗa a jihar Nasarawa, shi ne muke murnar wannan haɗin gwiwa.
"Wannan yana nufin ba kawai haraji za mu biya ba, amma jihar Nasarawa za ta rika samun rabo daga ribar da za mu samu,” in ji shi.
Mai ba da shawara na musamman ga gwamnan kan harkar noma, kuma manajan gonar shinkafar Jangwa, Mista Mohammed Iyimoga, ya gode wa gwamnan bisa goyon bayan da ya bayar, yana mai bayyana cewa sama da matasa 570 ne aka ɗauka aiki kai tsaye a gonar.

No comments