Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Kaduna Ta Ba El-Rufai Kwana Ɗaya Don Ya Bayar Da Shaida Ko Ya Ba Da Haƙuri Akan Zargin Biyan ‘Yan Ta’adda

…Ta buƙaci ya gabatar da hujja ko ya nemi afuwa a fili, ta kuma gargadi ɗaukar matakin shari’a. Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙaryata zargin da ...


…Ta buƙaci ya gabatar da hujja ko ya nemi afuwa a fili, ta kuma gargadi ɗaukar matakin shari’a.

Gwamnatin Jihar Kaduna ta ƙaryata zargin da tsohon Gwamna Nasir Ahmad El-Rufai ya yi cewa gwamnatin Gwamna Uba Sani ta biya ƴan bindiga Naira Biliyan ɗaya (₦1bn).

Gwamnatin ta bayyana kalaman da El-Rufai ya yi a wata hira da gidan talabijin na Channels a matsayin ƙarya, na siyasa, kuma marasa tushe ko wata shaidar da za ta tabbatar da su.

A wata sanarwa da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida, Dakta Sule Shu’aibu, SAN ya fitar, gwamnatin ta ce zargin El-Rufai “ƙirƙira ne marar ma’ana, marar tushe, kuma marar wani sahihancin da za a dogara da shi,” tana zarginsa da yunƙurin yaudarar jama’a da rage darajar ci gaban da aka samu wajen dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar.

Sanarwar ta kuma soki tsohon gwamnan kan “rashin tausayi wajen siyasantar da batun tsaro mai matuƙar muhimmanci,” tana mai cewa wannan dabi’ar ta yi ƙasa da abin da ake sa ran tsohon shugaba da ya taɓa rike madafun iko a jiha zai aikata.

Gwamnatin ta jaddada cewa Gwamna Uba Sani ba ya bayarwa, tattaunawa, ko biyan ko da kobo ɗaya ga kungiyoyin masu aikata laifuka. A cewar Kwamishinan, Gwamnan ya sha bayyana wannan matsayi a hira, taron manema labarai, da tattaunawa da masu ruwa da tsaki, yana mai nanata: “Ba naira ɗaya ba. Ba kobo ɗaya ba.”

Sanarwar ta kuma tunatar da cewa Ofishin Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara Kan Tsaro (ONSA) ya taɓa karyata makamancin wannan zargi da El-Rufai ya yi a baya, yana mai cewa ba Gwamnatin Tarayya ba, ko na jihohi, ke biyan kudin fansa ga miyagu.


Game da dabarun tsaro, gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa tana aiwatar da tsarin tsaro mai maida hankali kan al’umma, wanda ya ta’allaka kan ƙarfafa ayyukan soji, ƙara haɗin kai da sahihan shugabannin al’umma, da inganta samun ilimi, kiwon lafiya, da damar tattalin arziki. “Jihar na yin hulɗa da al’umma, ba da ƴan bindiga ba,”

Sanarwar ta kuma ambaci zarge-zargen da wasu manyan jami’an gwamnatin El-Rufai suka taɓa yi masa cewa ya yi amfani da kuɗaɗen jama’a wajen rarrashin wasu rukuni. Don haka, a cewar gwamnati, wannan sabon zargin nasa “lamari ne mai matuƙar ban mamaki.”

Tun hawansa mulki, Gwamna Sani ya mayar da hankali wajen kwantar da hankali a yankunan da suka fi rauni, sake buɗe makarantu, kasuwanni da gonaki, tare da gina sabuwar amana tsakanin al’ummomi da suka rabu a baya. Gwamnatin ta bukaci tsoffin jami’an gwamnati da su yi hattara da kalamai, su kuma mara wa ƙoƙarin zaman lafiya baya.

Sanarwar ta kalubalanci El-Rufai da ya gabatar da kowace irin shaida mai inganci—kamar bayanan banki, takardun cikin gida, ko bayanan tsaro dan yana da su. Ta kuma ce zarge-zargen da ya yi a watan Satumba 2025 ma bai taɓa gabatar da wata shaida a kai ba.

Gwamnatin ta bukaci El-Rufai ya janye maganarsa ya kuma bayar da cikakkiyar neman afuwa cikin mako guda, tana gargadi cewa rashin yin hakan zai tilasta wa jihar ɗaukar matakin shari’a “domin kare zaman jama’a da mutuncin hukumomi.”
 

No comments