Masu ruwa da tsaki a fannin lafiya a Jihar Kaduna sun yaba wa Gwamna Sanata Uba Sani bisa ƙoƙarin sa na sauya fasalin bangaren lafiya na jih...
Masu ruwa da tsaki a fannin lafiya a Jihar Kaduna sun yaba wa Gwamna Sanata Uba Sani bisa ƙoƙarin sa na sauya fasalin bangaren lafiya na jihar, ta hanyar gyaran asibitoci, samar da kayan aikin zamani, da kuma inganta walwalar ma’aikatan lafiyar.
Farfesa Bello Yusuf Jamoh, Babban Sakatare na Hukumar Kula da Lafiya a matakin Farko ta Jihar Kaduna, ya jaddada jajircewar gwamnan wajen zamanar da cibiyoyin lafiya da kuma inganta jin daɗin ma’aikatan lafiya domin ƙara inganta rayuwar al’ummar jihar Kaduna.
Yayin wani taron masu ruwa da tsaki, Farfesa Jamoh ya bayyana cewa ƙarin albashin ma’aikatan lafiya da aka yi kwanan nan zai ƙara ƙarfin bangaren, ya ƙara wa ma’aikata ƙwarin gwiwa, tare da ƙarfafa musu gwiwar yin aiki tuƙuru wajen yaƙi da cututtukan da ke kashe yara.
Haka kuma ya yaba da ci gaba da gyaran da kuma gina sababbin asibitoci, tare da samar da magunguna da kayan aiki na zamani, wadanda suka inganta yadda ake gudanar da ayyukan lafiya a fadin jihar.
Ya kuma yaba da Gidauniyar inshorar Lafiya ta Jihar Kaduna (KADCHMA) bisa rijistar jama’a cikin tsarin inshorar lafiya na jihar, da kuma yadda take taimaka wa mata wajen rungumar hanyoyin kariya daga cututtukan da ke kashe yara.
Farfesa Jamoh ya shawarci ma’aikatan lafiya da su ci gaba da kasancewa masu tsayawa a kan lokaci, jajircewa, da kuma bayar da kulawa mai inganci ga marasa lafiya, tare da kira ga jama’a da su rika amfani da cibiyoyin lafiya na matakin farko.
Dakta Yahuza Mohammed, shi ne jagoran ƙungiyar sakatarorin lafiya na jihar Kaduna, ya bayyana jin daɗinsa da irin sauye-sauyen da aka samu, tare da tabbatar wa hukumar cewa za su karfafa gwiwar Ƙananan Hukumomi domin tabbatar da cewa ma’aikata sun nuna bajinta da amincewar gwamnati ta hanyar sadaukar da kai a aiki.
Comrade Umar Ibrahim Patika, shugaban ƙungiyar ’yan jarida a fannin lafiya ta jihar Kaduna, ya yaba wa Gwamna Uba Sani bisa fifita walwalar ma’aikatan lafiya, yana mai cewa, farin cikin da ake gani a tsakanin ƙwararru ya nuna irin tasirin shugabancin gwamnan.
“Muna yaba wa gwamnan bisa jajircewarsa da sadaukar da kai wajen inganta rayuwar dukkan ma’aikatan jihar Kaduna,” in ji Patika.
Shugaban sashen sadarwa da dabarun ƙungiyar masu kare muhalli ta Afrika (African Climate Reporters), Comrade Ibrahima Yakubu, shi ma ya jinjinawa gwamnan bisa yadda ya canja tsarin kula da lafiya a jihar.


No comments