Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

TALLAFIN KARATU: Ɗaliban Da Ke Koyon Lauya Sun Yaba Wa Gwamnan Kano

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An yaba wa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa tun da ake bayar da tallafi ga ɗaliban da ke koy...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An yaba wa Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf da cewa tun da ake bayar da tallafi ga ɗaliban da ke koyon aikin Lauya 'Law'a jihar Kano ba a taba samun wata gwamnati da ta tsaya tsayin-daka wajen tallafa musu kamar Gwamnatin sa ba.

Ɗaya daga cikin ɗalibai masu karantar Shari'a  ɗan asalin jihar Kano, Mustapha Dandinshe ne ya wannan yabin, inda ya bayyana cewa Gwamnatin jihar Kano ta zama abar misali wajen nuna kulawa ga ci gaban ilimi, musamman irin tallafi da ake bai wa ɗalibai na fannin shari’a.

Sai dai Mustapha Isah Dandinshe ya koka da cewa a wannan karon suna ɗan fuskantar jinkiri na tallafin karatun da ake ba su a wannan yanayi da dlɗaliban Kano da ke' Law School" ke cikin buƙatar gaggawa na tallafin don ci gaba da karatun su ba tare da tangarda ba.

Don haka ɗalibai masu karatu a sassa daban-daban a faɗin Nijeriya suke roƙon Gwamnan da mataimakin sa, wanda shi ne Kwamishinan ilimi na manyan makarantu su duba buƙatunsu.
 

No comments