Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

MAULUD: Shugabar Matan Kwankwasiyya Ta Saudiyya Ta Tallafa Wa Gajiyayyu

Daga Ibrahim Muhammad ,Kano A ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi da ta ke yi, shugabar matan Kwankwasiyya ta Saudi Arebiya, wacce ta ke ...


Daga Ibrahim Muhammad ,Kano

A ci gaba da gudanar da ayyukan alkhairi da ta ke yi, shugabar matan Kwankwasiyya ta Saudi Arebiya, wacce ta ke kuma babbar mataimakiya ta musamman ga shugaban Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, Hon. Salim Hashim akan Kasuwanci da hannun jari,  ta kai ziyara gidan gajiyayyu na Shahuci, tare da raba musu tallafi domin murnar Maulidinnabiy.

Hajiya Mariya ta kai ziyarar ne tare da bayar da kayan tallafin ga gajiyayyu da masu larurar rashin lafiyar ƙwaƙwalwa domin murnar zagayowar watan da aka haifi Manzon Allah (SAW)

Hajiya Mariya Ali Zage  ba ta tsaya nan ba, sai da  ta kai makamanciyar wannan ziyarar a Asibitin  Æ™wararru na Murtala Muhammad da ke cikin birni na Kano, inda ta duba marasa lafiya kuma ta yi musu addu'ar samun sauÆ™i da raba musu kayan masarufi.

Jami'ai masu kula da gidan gajiyayyu na Shahuci da na Asibitin ƙwararru na Murtala sun yaba da wannan irin kulawa na nuna jin ƙai da tausayi da taimako, wanda shugabar matan ta Kwankwasiyya ke yi, tare da yin kira ga sauran al'umma su kwaikwaya daga irin wannan halaye masu nagarta.

A nata jawabin, Hajiya Mariya Ali Zage ta ce wannan irin gudumawar da ta ke bayarwa, kwaikwayo ne daga irin halayyar da jagoran su na Kwankwasiyya, Dakta Rabiu Musa Kwankwaso ya É—ora su a kai, da kuma koyi ga irin kulawa da suka ga Gwamna Abba Kabir ke yi na taimaka wa jama'a  musamman masu Æ™aramin Æ™arfi.
 

No comments