Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Shugaba Tinubu Ya mayar Da Ofishin Kwamitin Bada Afuwa Zuwa Ma’aikatar Shari’a, Tare Da Yin Afuwa Ga Wasu Fursunoni

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan takardun bada afuwa da sassauci ga wasu mutane da aka yanke wa hukunci bisa laifuka daban...


Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan takardun bada afuwa da sassauci ga wasu mutane da aka yanke wa hukunci bisa laifuka daban-daban, a wani mataki na aiwatar da ikon sa na yin afuwa bisa kundin tsarin mulkin Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai, Bayo Onanuga, ya fitar ranar Talata, shugaban ya ce ya ɗauki matakin ne bayan tuntubar majalisar ƙoli ta ƙasa da kuma bayan samun ra’ayoyin jama’a kan batun.

Sai dai bayan sake duba jerin sunayen waɗanda za su ci gajiyar afuwar, an cire waɗanda aka samu da manyan laifuka, irin su garkuwa da mutane, safarar miyagun ƙwayoyi, cinikin mutane, zamba, da mallakar makamai ba bisa ƙa’ida ba.

A cewar fadar shugaban ƙasar, wannan matakin ya zama dole saboda laifukan da suka shafi tsaro da tasirin su ga al’umma, da kuma buƙatar kare haƙƙin waɗanda aka zalunta da ƙarfafa gwiwar hukumomin tsaro.

Sanarwar ta ƙara da cewa an tura sabuwar takardar sunayen waɗanda suka cancanci afuwa zuwa hukumar kula da gidajen gyaran hali domin aiwatar da shi.

Shugaba Tinubu ya kuma bayar da umarnin mayar da ofishin sakateriyar kwamitin bada afuwa daga ma’aikatar ayyuka na musamman zuwa ma’aikatar shari’a ta tarayya.

Bugu da ƙari, ya umarci babban lauyan ƙasa, da ya fitar da sabbin ƙa’idojin da za su jagoranci tsarin bada afuwa nan gaba, ciki har da shawarwari da hukumomin shari’a kafin ɗaukar mataki.

Shugaban ƙasar ya gode wa jama’a da masu ruwa da tsaki bisa shawarwari da suka bayar, tare da tabbatar da ƙudirin gwamnatin sa na inganta tsarin shari’a da tabbatar da adalci a Nijeriya.















 

No comments