Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SAMAR DA AYYUKAN YI: Gwamnatin Tarayya Za Ta Zuba Jarin Dalar Amurka Miliyan 220 — Shettima

Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin zuba jarin Dalar Amurka miliyan 220 domin samar da sabbin damammakin ayyukan yi ga matasan ƙasara nan. ...


Gwamnatin Tarayya ta sanar da shirin zuba jarin Dalar Amurka miliyan 220 domin samar da sabbin damammakin ayyukan yi ga matasan ƙasara nan.

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ne ya bayyana haka a ranar Laraba yayin ƙaddamar da shirin Nigeria Jubilee Fellows Programme (NJFP) 2.0 a Fadar Shugaban Ƙasa da ke Abuja.

Shirin, wanda aka haɗa gwiwa da Tarayyar Turai (EU) da Asusun Raya Ƙasashe na Majalisar Ɗinkin Duniya (UNDP), na nufin haɗa matasa masu ƙwarewa da dama ta fannin horo, gogewa da kuma jagoranci (mentorship), domin taimaka musu su shiga sahun masu dogaro da kai.

Shettima ya ce burin gwamnati shi ne rage tazara tsakanin karatu da samun aiki, ta hanyar bai wa matasa damar amfani da ilimin da suka samu wajen gina tattalin arziƙin ƙasa.

Ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Bola Tinubu za ta tabbatar da cewa shirin ya samu tallafi kai tsaye daga kasafin kuɗi na ƙasa, tare da buɗe “NJFP Basket Fund” domin samar da hanyoyin samun kuɗaɗen da za su dore.

Mataimakin shugaban ƙasar ya yi kira ga masu zuna jari masu zaman kansu, ƙungiyoyin ci gaba da masu ba da gudummawa su haɗa kai wajen tabbatar da nasarar shirin.

Ya bayyana cewa gwamnati za ta tabbatar da adalci da haɗin kai wajen aiwatar da mataki na biyu na shirin, domin ya shafi matasa daga kowane yanki da bangare na ƙasa, musamman a fannoni kamar noma, makamashi, fasahar zamani, masana’antu da kuma harkokin kirkire-kirkire.

Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, ya bayyana NJFP 2.0 a matsayin ci gaba daga nasarorin da aka samu tun 2021, inda sama da matasa 13,000 suka amfana da horo da ayyuka.

Ya ce gwamnati na da burin samar wa matasa 100,000 aiki cikin shekaru biyar masu zuwa.

Jakadiyar UNDP a Najeriya, Ms Elsie Attafuah, ta ce haɗin gwiwar da ake da EU da UNDP ta samar da damammaki da ta kai sama da matasa 40,000 cikin fannoni daban-daban na tattalin arziƙi.

Ita ma jakadiyar Tarayyar Turai a Najeriya, Gauthier Mignot, ta ce EU na fatan ganin NJFP 2.0 ya zama ɓangare na tsarin gwamnati, domin tabbatar da dorewarsa.







 

No comments