Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnan Kaduna Ya Amince Da Ƙarin Albashin Ma’aikatan Manyan Makarantun jihar Kaduna

Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da aiwatar da ƙarin albashi na kashi 70 cikin 100 bisa sabon tsarin albashi ga ma’aikatan d...


Gwamnan Jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya amince da aiwatar da ƙarin albashi na kashi 70 cikin 100 bisa sabon tsarin albashi ga ma’aikatan dukkan manyan makarantu mallakar jihar, wanda  za a fara aiwatarwa daga watan Oktoba, 2025.

Amincewar ta biyo bayan ganawa da aka gudanar tsakanin gwamnan da shugabannin ƙungiyar haɗin gwiwar ma’aikatan manyan makarantu (JUTIKS), wanda hakan ya kai ga dakatar da yajin aikin da suka fara tsawon wata guda.

An gudanar da ganawar ne a gidan gwamnatin Kaduna, ƙarƙashin jagorancin ƙungiyar ƙwadago ta Nijeriya (NLC), reshen Kaduna, inda wakilai daga kwalejin Nuhu Bamalli da  Kwalejin Ilimi ta Gidan Waya, da Kwalejin Koyar da Unguwar Zoma.

Ƙungiyoyin sun fara yajin aiki ne tun ranar 30 ga Satumba, 2025, domin neman aiwatar da tsarin albashi na 2009 ( CONPCASS/CONTEDISS) inganta fansho, da kuma walwalar ma’aikata gaba ɗaya.

A wani taron manema labarai da aka gudanar bayan ganawar, shugabannin ƙungiyoyin sun yaba da jagoranci, gaskiya da jajircewar Gwamna Sani wajen inganta harkar ilimi da kare haƙƙin ma’aikata, kamar yadda aka bayyana cikin sanarwar da shugaban ƙungiyar ƙwadago ta Kaduna,  Kwamared Ayuba Suleiman da na  (JUTIKS/ASUP), Kwamared  Usman Shehu Suleiman, tare da Sakatare Janar na (JUTIKS) Kwamared Shuaibu Dauda Adamu da Shugaban (COESU,) Kwamared Nuhu Yerima Christopher da Shugaban (NASU) Kwamared Aliyu Ƙwarbai; da Shugaban ƙungiyar Malamai,  Kwamared Daniel Danboyi, suka sanyawa  hannu.

Sun tabbatar da muhimman abubuwan da aka cimma matsaya a kan su, waɗanda suka haɗa da aiwatar da kashi 70 cikin 100 na tsarin albashi na 2024 ga malamai da ma’aikata marasa koyarwa, da kuma amincewa da shekaru 65 a matsayin shekarun ritaya da kuma shekaru 40 na aikin gwamnati ga ma’aikata marasa koyarwa.

Rahotanni sun gano cewa kafin wannan ƙarin albashi, mafi yawan ƙananan malamai suna karɓar kimanin N64,000 a kowane wata bayan cire kuɗaɗen da ake cirewa.
 

No comments