Daga Hussaini Yero, Gusau Ƙungiyar Mata manoma ta Nijeriya (NAWIA), reshen Zamfara ta tallafa wa mata 114 da ƙungiyoyin mata 6 da kayan aiki...
Daga Hussaini Yero, Gusau
Ƙungiyar Mata manoma ta Nijeriya (NAWIA), reshen Zamfara ta tallafa wa mata 114 da ƙungiyoyin mata 6 da kayan aikin gona a jihar Zamfara.
Shugabar ƙungiyar NAWIA ta jihar, Hajiya Shemau Nalado ce ta raba kayan tallafin ga mata manoma a wani taron tunawa da ranar abinci ta duniya da aka gudanar a Gusau cikin makon danya gabata.
Shema'u Nalado ta bai wa mata manoma 70 kayan shuka, iri na Shinkafa da na waken soya, takin zamani, maganin ciyawa da kuma maganin ƙwari.
Hakazalika,ta ba mata 30 masu matsakaitan sana’o’i da suka haɗa da Wara, waina, an ba kowacce daga cikin su buhun gawayi, man suya, da kilo 10 na Shinkafa da litar man girki.
Kuma ga ƙungiyoyi shida mata manoma kowacce za ta karbi fanfunan feshi, famfun ruwa, na’urar tuka wutar lantarki da kuma maganin feshin ciyawa".
Shemau ta ƙara da cewa, kayayyakin da aka raba an samo su ne daga gudumawar da gwamnati da sauran abokan hular da ungiyoyi.
Hajiya Shema'u ta yaba da ƙaruwar adadin mata a harkar noma, tana cewa mambobin da suka yi rajista da NAWIA a yanzu sun haura 2000, yayin da waɗanda ba su yi rajista ba sun kai 5,000.
Shemau ta kuma miƙa godiyar ta ga Uwargidan gwamnan jihar Zamfara, Hajjiya Hurriya Dauda bisa namijin ƙoƙarin da ta ke yi na bunƙasa noman mata a Jihar Zamfara.
"Sauran hukumomi da ƙungiyoyin da muke tare,sun hada da, Zamfara Chambers of Commerce, ACRESAL, NG-CARES, LIPAN LP PRESS da kuma Nigeria Export Promotion Council (NEPC)," ta ce.
A jwabin ta, Uuwargidan gwamnan jihar Zamfara Hajjiya Huriya Lawal, da ta samu wakilcin Barista Rukayyat Mani, Uwar gidan maimakin Gwamna, ta bayyana cewa, taken bana na ranar Abinci na Duniya shi ne “hannu da hannu don samar da ingantacciyar abinci da kyakkyawar makoma,” ta bukaci hadin kai tsakanin manoma da iyalai da shugabanni domin samar da abinci mai inganci ga kowa da kowa.
Uwargidan gwamnan Zamfara, ta ce haɗa hannu da ƙungiyoyi irin su NAWAIA zai ci gaba da tabbatar ci gaban manoma mata a Zamfara.
Ta ce, “Yayin da muke murnar wannan rana ta musamman, ina kira ga manoma musamman mata manoma da su ci gaba da yin aiki tuƙuru, kada su yi ƙasa a gwiwa, ku ne ƙarfin jihar mu kuma ginshikin samar da abinci a kasarmu.
"Za mu yi aiki kafaɗa da kafaɗa da gwamnati, da kamfanoni masu zaman kansu, da al'umma sun mai da jihar Zamfara ta zama abin koyi na wadatar abinci, tsayin daka, da fata ga daukacin al'umma.

No comments