Jam’iyyar NNPP a jihar Kaduna ta ƙaryata rahoton da ake yadawa cewa an tsige Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Mohammed Lawal Sultan, wa...
Jam’iyyar NNPP a jihar Kaduna ta ƙaryata rahoton da ake yadawa cewa an tsige Shugaban jam’iyyar na jihar, Alhaji Mohammed Lawal Sultan, wanda wasu da aka kora daga jam’iyyar suka sanar.
Shugabancin jam’iyyar ya bayyana cewa, waɗanda suka yi wannan sanarwar na ƙarya an kore su daga jam’iyyar tun da daɗewa saboda ayyukan da suka saba wa jam’iyya da kuma haɗa kai da ‘yan adawa.
A cikin wata sanarwa da Sakataren Jam'iyyar na jihar Kaduna, Alhaji Zubairu Hassan Mai Anguwa, ya fitar, ya ce waɗanda suka ɗauki nauyin wannan sanarwa ba su kasance mambobin jam’iyyar ba, na tsawon lokaci.
Ya ce shugabancin jam’iyyar ya shigar da ƙorafi ga ‘yan sanda da kuma hukumar DSS kan abin da ya kira sojan gona da karkatar da kudaɗen jam'iyyar wanda aka tara yayin sayen fom na 'yan takara. Ya kuma kuma ƙarya ta iƙirarin zama mambobin jam’iyyar da wasu mutane biyu suka aikata Jumare Tanimu Magaji da Joshua Madaki.
“Ina so in fayyace cewa waɗannan mutanen da suka ce sun tsige shugaban, an kore su daga jam’iyyar tun da dadewa saboda ayyukan da suka saba wa jam’iyya da kuma hada kai da ‘yan adawa domin su haifar da rikici a cikin NNPP,” in ji shi.
Ya tabbatar da cewa jam’iyyar NNPP a Kaduna ta na cikin haɗin kai da zaman lafiya, inda ya bayyana batun tsige shugaban a matsayin yunƙurin ƙirƙirar rikici da tashin hankali a cikin jam’iyyar.
Akan hakan tace tuni shugabancin jam'iyyar ya kafa kwamitin bincike donin gano yadda kudadan suka salwanta wanda hakan ya sanya suka fara neman hanyar kawowa jam'iyyar matsala.

No comments