Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar mai a ƙauyen...
Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) ta tabbatar da cewa adadin mutanen da suka rasa rayukansu sakamakon fashewar tankar mai a ƙauyen Essa, kan hanyar Bida–Badeggi–Agaie da ke cikin Ƙaramar Hukumar Katcha ta Jihar Neja, ya haura zuwa mutane 45.
Shugaban ofishin NEMA na Minna, Hussaini Isah, wanda ke kula da jihohin Neja da Kwara, ya bayyana hakan a cikin rahoton halin da ake ciki da ya fitar ranar Juma’a.
Ya ce fashewar ta faru ne bayan tankar mai ta gamu da wata mummunar karyewar hanya, wanda ya haddasa hatsarin. Ya bayyana ƙauyen Essa a matsayin wurin da aka fi samun barna.
“Yanzu jimillar waɗanda suka mutu ta kai 45, ciki har da maza 12, mata 27, da yara 6.
Sannan an ji rauni ga mutane 63 — maza 24, mata 32, da yara 7,” inji Isah.
Ya bayyana cewa duk waɗanda abin ya rutsa da su sun kasance masu ɗibar mai daga tankar da ta kife, kafin ta fashe.
Wasu daga cikin waɗanda suka jikkata sun samu taimakon gaggawa a Cibiyar Kiwon Lafiya ta Farko ta Essa da Asibitin Idris Private Hospital, kafin daga baya a mayar da su Asibitin Gwamnati na Umaru Sanda, Bida, da kuma Cibiyar Lafiya ta Ƙasa (FMC), Bida.
Daga cikin waɗanda suka fi tsananin rauni, mutum 14 an tura su zuwa Asibitin Kwararru na Gwagwalada a birnin Abuja domin samun kulawa ta musamman.
Isah ya ƙara da cewa hukumomi daban-daban na gaggawa sun halarci wurin domin taimakawa ceto da kashe gobara, ciki har da ‘yan sanda, DSS, NSCDC, FRSC, da ma’aikatan NEMA, tare da ‘yan sa kai da mazauna yankin.
Ya bayyana cewa Gwamnatin Jihar Neja ta tura magunguna da kayan agaji zuwa asibitocin da abin ya shafa, yayin da wasu daga cikin marasa lafiyar suka sallami kansu bayan samun kulawa.
Sai dai kuma, ya ce wasu mutane 12 da aka fara ba su taimako a gida sun sake komawa asibiti domin samun cikakkiyar kulawa.
Isah ya koka da cewa cinkoson ababen hawa, lalacewar hanya, da kuma matsalar sadarwa, sun kawo tsaiko a ayyukan ceto da haɗin gwiwar jami’an tsaro a wurin.
.jpg)
No comments