Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Muna Fata Za A Faɗaɗa Taron Nuna Al'adu A Dukkan Ƙananan Hukumomin Kano, In ji Daraktan Mulki Na Kabo

Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana taron nuna al'adu da Gwamnatin jihar Kano ta shirya da cewa abu ne mai kyau domin yara da suke ta...


Daga Ibrahim Muhammad, Kano

An bayyana taron nuna al'adu da Gwamnatin jihar Kano ta shirya da cewa abu ne mai kyau domin yara da suke tasowa su san al'adarc su, Mutum ya san daga ina yake, ina za shi, abubuwa ne da yawa aka gabatar har da tambayoyi da wasa ƙwaƙwalwa domin sanin abubuwa na al'ada masu kyau da wasu basu sani ba, inda ake fatan za a faɗaɗa shirin zuwa dukkan Ƙananan Hukumomin jihar Kano.

Alhaji Nazifi Ado Shitu, Daraktan mulki na Ƙaramar Hukumar Kabo ne ya bayyana hakan a madadin shugaban Ƙaramar Hukumar Kabo. Hon. Lawan Najume a wurin taron nuna al'adu da da ke gudana yanzu haka a Kano.

Ya ce akwai abubuwa da suka taso suka gani  ana yin su a Ƙananan Hukumomi na wasannin Fulani da na Hausawa, irins u shaɗi, langa da  saka zare da allura da baya da bazai matan ba a  tsohuwar Dambatta a ƙofar gidan Marigayi Sarkin Bai, Halkimin Dambatta suna zuwa kallon irin wannan wasa .

Ya ce, irin wannan taro na kalankuwa zai taimaka wajen farfaɗo da al'adun mu na gargajiya. Kuma yana da kyau a riƙa shiryawa ana yi a hedukwatar Ƙananan Hukumomi.

Daga nan ya gode wa Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf da ma'aikatar raya al'adu da yawon buɗe ido, da kwamitin shirya taron ƙarƙashin mataimakin Gwamnan jihar Kano, wanda shirya taron da shi ne karo na farko kuma suna fata za a faɗaɗa nan gaba a riƙa yi a kowace Ƙaramar Hukuma.

Daraktan ya ce, Ƙaramar hukumar Kabo ƙarƙashin jagorancin Hon. Lawan Najume ta zo ta baza Kolin irin kayan ta da ta ke yi na gargajiya, waɗanda suka haɗa da tukwane na ƙasa da asusun tara kuɗi, da abinci na gargajiya da ake yi a da, kuma har yanzu ana amfani da su a tsakanin al'umma.
 

No comments