Daga Khalid Idris Doya Duk da barazanar da Ƙabilar Sayawa da ke Ƙaramar Hukumar Tafawa Balewa suka yi na nuna adawa da duk wani wanda za a ...
Daga Khalid Idris Doya
Duk da barazanar da Ƙabilar Sayawa da ke Ƙaramar Hukumar Tafawa Balewa suka yi na nuna adawa da duk wani wanda za a naɗa masu a matsayin Sarki, in ba wanda su ke so ba, Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad ya tabbatar da naɗin Burgediya Janar Marcus Kokko Yake (Mai ritaya) a matsayin sabon Sarkin Ƙabilar Sayawa (Gung Zaar) a kan matakin Sarki mai darajata ta ɗaya, sabanin wanda suke so, wato Air Commodore Ishaku Komo (Mai ritaya).
Da ya ke jawabi bayan amsar takardar zama Sarkin masarautar Sayawa a ranar Litinin, Zaɓaɓɓen Gung Zaar ya yi alƙawarin gudanar da shugabanci mai cike da adalci domin wanzar da zaman lafiya da haɗin kai a tsakanin al'ummar Sayawa.
Marcus Kokko Yake ya gode wa gwamnan jihar Bala Muhammad bisa naɗin da ya masa tare da bayar da tabbacin yin mulki na kwarai tare da sadaukar da kai domin jama'arsa.
Daga nan ya roƙi haɗin kai da goyon bayan sarakuna, al'umma da shugabanni domin kyautata zaman lafiya da cigaban Sayawa da ma jihar Bauchi baki ɗaya.
Da ya ke gabatar masa da takardar naɗin nasa, sakataten gwamnatin jihar Bauchi, Alhaji Aminu Hammayo, ya taya sabon Sarkin murna tare da kira a gareshi da tabbatar da bin dokokin jihar da na ƙasa da yi wa jama'a hidima.
Ya kuma tunatar da shi kan biyayya wa ƙa'idojin gwamnati tare da nemansa da ya yi aiki sosai domin wanzar da zaman lafiya, adalci da ci gaban masarautarsa.
Hammayo ya ce naɗin da aka yi an duba cancanta ne da kuma kyakkyawar tarihin da sabon Gung ɗin ke da shi.
In dai ba a manta ba, a makon da ya gabata mun kawo maku wata zanga-zanga da al'ummar Sayawan suna gudanar, ina a ciki aka ji wata murya tana cewa, in dai ba Air Commodore Ishaku Komo aka naɗa masu a matsayin Sarki (Gung Zaar) ba, to babu zaman lafiya a Tafawa Balewa.







No comments