Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Jami'ar ABU Zaria Ta Ƙaryata Zargin Tsunduma Cikin Shirye-shiryen Ƙera Makamin Nukiliya

Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) ta bayyana cewa ba ta da wani hannu a cikin duk wani shiri na ƙera makamin nukiliya a Nijeriya, tana...



Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya (ABU) ta bayyana cewa ba ta da wani hannu a cikin duk wani shiri na ƙera makamin nukiliya a Nijeriya, tana mai bayyana wani faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke zarginta da hakan a matsayin ƙarya tsantagwaro.

A cewar Daraktan Sashen Hulɗa da Jama’a na jami’ar, Auwalu Umar, wanda ya fitar da sanarwa ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a ranar Asabar, bidiyon da aka ƙirmira ta hanyar fasahar AI (Artificial Intelligence) na ƙoƙarin yaudaran jama’a kan shirye-shiryen makamashin nukiliya na ƙasa.

Umar ya bayyana cewa bidiyon ya yi ƙarya da ikirarin cewa masana kimiyya na Najeriya tun a shekarun 1980 sun ɓoye wani shiri na tace uranium mai ƙarfi a Kaduna tare da taimakon cibiyar bincike ta ABU, inda ake zargin sun samu kayan aikin “centrifuge” daga shahararren ɗan Pakistan, A.Q. Khan.

Ya ce wannan labari babu tushe, babu makama, kuma ba shi da wata hujja da za ta tabbatar da sahihancinsa.

“Yawancin masana kimiyya na ABU da ke Cibiyar Bincike kan Makamashin Nukiliya (CERT) a wancan lokaci, suna ci gaba da karatu ne a ƙasashen waje, don haka ba su da wata dama ko damar shiga irin wannan aiki na tace uranium,” in ji Umar.

Daraktan ya ƙara da cewa jami’ar ba ta da wata alaƙa da AQ Khan ko kuma wani tsarin da ya shafi samar da kayan aikin kera makamin nukiliya, kuma babu wata na’ura ta centrifuge da ta taɓa shiga jami’ar.

Ya bayyana cewa kafin shekara ta 1987, kadai ne tsarin makamashin nukiliya da jami’ar ke da shi shi ne “14 MeV Neutron Generator”, wanda aka fara amfani da shi a 1988.

“Nijeriya ta samu na’urar nukiliya ta farko (NIRR-1) ne a 1996 ta hannun Hukumar Makamashin Nukiliya ta Duniya (IAEA), wacce aka kaddamar da ita a 2004,” in ji shi.

Umar ya jaddada cewa duk ayyukan nukiliya a Najeriya suna bisa tsarin zaman lafiya, tare da bin ƙa’idar yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya (NPT) da yarjejeniyar Pelindaba, waɗanda suka haramta kera irin waɗannan makamai.

Ya kuma bayyana cewa cibiyar binciken makamashin nukiliya ta ABU tana aiki ne cikin haɗin gwiwa da ƙasashe kamar Amurka, Rasha, da China, tare da kulawar IAEA.

“ABU ba ta taɓa shiga wani shiri na sirri da ya shafi makamin nukiliya ba. Tun asali, jami’ar ta himmatu wajen amfani da kimiyyar nukiliya domin ci gaban ƙasa da taimakon ɗan adam,” inji Umar.

Ya ƙara da cewa Sir Ahmadu Bello, wanda ya kafa jami’ar, tun a 1960 bayan ziyarar da ya kai Cibiyar Bincike ta Oak Ridge a Amurka, ya nuna sha’awar amfani da makamashin nukiliya cikin zaman lafiya — kafin a kafa jami’ar shekaru biyu bayan nan.

A ƙarshe, jami’ar ta nanata aniyarta na ci gaba da gudanar da binciken kimiyya cikin gaskiya da amana, tare da tabbatar da cika dukkan alƙawuran ƙasa da na duniya wajen tabbatar da amfani da makamashin nukiliya cikin natsuwa da lumana.

No comments