Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Majalisar Dokokin Nijeriya Ta Fara Tattaunawa Kan Ƙirƙirar Sabbin Jihohi 55 Da Ƙananan Hukumomi 278

Majalisar Dokokin Nijeriya ta fara nazari kan muhimman sauye-sauyen Kundin Tsarin Mulki da ka iya haifar da ƙirƙirar sabbin jihohi 55 da kum...



Majalisar Dokokin Nijeriya ta fara nazari kan muhimman sauye-sauyen Kundin Tsarin Mulki da ka iya haifar da ƙirƙirar sabbin jihohi 55 da kuma ƙananan hukumomi 278 a faɗin ƙasar.

Rahotanni sun bayyana cewa Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin (APC, Kano Ta Arewa), ne ya bayyana hakan a wani taron bita na hadin gwiwa tsakanin majalisar dattawa da ta wakilai kan sake duba Kundin Tsarin Mulki da aka gudanar a Legas na tsawon kwana biyu.

A cewar mai magana da yawunsa, Ismail Mudashir, Sanata Barau ya sake jaddada cewa majalisar ta kuduri aniyar kawo gyare-gyare masu maida hankali kan bukatun jama’a tare da tabbatar da cewa an mika kashi na farko na sauye-sauyen kundin tsarin mulki zuwa majalisun dokoki na jihohi kafin ƙarshen wannan shekara.

“Mun shafe kusan shekaru biyu muna aiwatar da wannan tsari — muna tattaunawa da al’ummomi, kungiyoyin farar hula, hukumomi, da ƙungiyoyin ƙasa domin tattara ra’ayoyi da shawarwari. A yau muna da abubuwa 69 da suka haɗa da bukatun ƙirƙirar jihohi 55, gyaran iyaka guda biyu, da ƙirƙirar ƙananan hukumomi 278,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, ‘yan majalisa suna da alhakin tattauna da warware waɗannan shawarwarin kafin gabatar da rahoton su ga zauren majalisar, yana mai nuna fatan cewa za a cimma gagarumar nasara cikin kwanaki biyu na taron.

“Ba ƙaramin aiki ba ne wanda za mu iya kammala cikin kwanaki biyu, amma ina da tabbacin za mu iya yi, musamman tunda mun yi alkawarin mika gyaran farko kafin ƙarshen shekara,” inji Sanata Barau.

Ya bukaci mambobin kwamitin da su guji son zuciya da rikice-rikicen siyasa, yana mai jan hankalin su da cewa wannan aikin ya shafi moriyar ƙasa gaba ɗaya, ba wani ɓangare na musamman ba.

“Muna nan a matsayin kwamitin guda ɗaya; bai kamata mu rarrabu zuwa ‘mu’ da ‘su’ ba. Dole mu yi aiki bisa moriyar ‘yan Najeriya gaba ɗaya,” inji shi.

Ya ƙara da cewa, an shirya wannan bita ne domin samar da shawarwari da suka dace da tanadin Sashe na 9 na Kundin Tsarin Mulki, wanda ke tsara yadda ake aiwatar da gyare-gyare a tsarin mulkin ƙasa.

No comments