Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar ƙoƙarin da wasu ƙasashe suke yi na neman wargaza haɗin k...
Gwamnatin Tarayya ta yi kira ga ‘yan Nijeriya da su haɗa ƙarfi da ƙarfe wajen yaƙar ƙoƙarin da wasu ƙasashe suke yi na neman wargaza haɗin kan ƙasar nan ta hanyar yaɗa labaran ƙarya da bayanai marasa tushe.Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya yi wannan kira a ranar Talata lokacin da ya karɓi baƙuncin Buɗaɗɗiyar Jami’ar Nijeriya (National Open University of Nigeria, NOUN) ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Olufemi Peters, a wata ziyarar ban-girma da suka kai ofishin sa da ke Abuja.
Idris ya ce: “Ya kamata ‘yan Nijeriya su haɗa kai domin daƙile labaran ƙarya da ake yaɗawa game da ƙasar mu. Dukkan mu muna da alhakin bayyana gaskiya da kare mutuncin Nijeriya. Labaran ƙarya na iya haifar da rarrabuwar kawuna a ƙasa, kuma dole ne mu hana hakan faruwa a tamu ƙasar.”
Ya kuma bada tabbacin cewa Gwamnatin Tarayya tana ci gaba da jajircewa wajen inganta ilimin kafofin watsa labarai domin bunƙasa faɗin gaskiya, kawo haɗin kai, da cigaban ƙasa.
Ministan ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa wajen yaƙar yaɗuwar labaran ƙarya, yana mai cewa irin waɗannan labaran suna iya shafar zaman lafiya, haɗin kai, da mutuncin ƙasa gaba ɗaya.
Ya yaba wa jami’ar NOUN bisa yadda ta kafa tarihi wajen bunƙasa tsarin koyarwa daga nesa, da kuma shirin ta na gudanar da sabuwar Cibiyar Ilimin Kafofin Watsa Labarai ta Ƙasa da Ƙasa (IMILI), wadda ake sa ran za ta samu takardar shaida a taron UNESCO da za a yi a birnin Samarƙandi na ƙasar Uzbekistan, cikin Nuwamba 2025.
Idris ya ce: “IMILI ba kawai wata cibiyar ilimi ba ce, har ma babban jarin ƙasa ne da aka zuba kan tabbatar da gaskiya, ilimi, da wayar da kai. Shi ya sa Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai take aiki tare da NOUN, UNESCO, da Ma’aikatar Ilimi domin tabbatar da an amince wa Nijeriya ta gudanar da wannan cibiya a taron UNESCO da ke tafe.”
Ya ƙara da cewa manufar IMILI ita ce inganta ayyukan kafafen yaɗa labarai da kuma ƙarfafa matsayin Nijeriya a duniya wajen ilimin kafofin watsa labarai, wanda ya yi daidai da Ajandar Sabunta Fata ta Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, wadda ta ƙunshi tsare gaskiya, riƙon amana, da wayar da kan jama’a.
A nasa ɓangaren, Mataimakin Shugaban NOUN, Farfesa Olufemi Peters, ya bayyana godiyar sa ga Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai bisa yadda ta amince wa jami’ar ta gudanar da cibiyar IMILI, yana mai cewa Gwamnatin Tarayya ta bayar da tallafin naira miliyan 250 domin kafa cibiyar.
Farfesa Peters ya bayyana IMILI a matsayin wani muhimmin mataki da zai ƙarfafa jagorancin Nijeriya a fagen ilimin kafofin watsa labarai a duniya, inda ya sha alwashin cewa NOUN za ta ci gaba da jajircewa wajen tabbatar da nasarar cibiyar da samun amincewar ƙasashen duniya gare ta.
Ya ce: “Jami’ar NOUN ta shirya tsaf wajen tabbatar da samun sahalewar ƙasashe ga cibiyar IMILI a matsayin Cibiyar UNESCO ta rukuni na biyu, kuma wannan zai ƙara ɗaukaka martabar Nijeriya a fagen ilimi da ilimin kafofin watsa labarai.”
Ya tabbatar da cewa jami’ar tana da kayan aiki na zamani, ƙarfin gudanarwa, da ƙwarewar malamai, waɗanda za su tabbatar da ɗorewar cibiyar tare da tabbatar da ’yancin ta da dacewar ta a matakin ƙasa da ƙasa.

No comments