Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu akan sababbin dokokin haraji guda huɗu, waɗanda suka tsallake karatu a Majalisar Dokoki na Ƙasa a baya. ...
Shugaba Bola Tinubu ya sanya hannu akan sababbin dokokin haraji guda huɗu, waɗanda suka tsallake karatu a Majalisar Dokoki na Ƙasa a baya.
Shugaban ƙasar ya yi haka ne a Fadar Shugaban Ƙasa dake Abuja, inda aka samu halarcin jagorancin majalisa da wasu ƴan majalisu da gwamnoni da ministoci da mataimakan Shugaban Ƙasa.
Ƙudirorin sun haɗa da na haraji na Ƙasa, na tattara haraji na Ƙasa, na samar da hukumar kuɗaɗen haraji da kuma na samar da hukumar haɗaka ta haraji, waɗanda aka tantance su a Majalisar Dokoki ta Ƙasa biyo bayan nazari mai zurfi da shawartar masu-ruwa-da-tsaki.
Ana sa ran hakan zai taimaka wajen sauya tsarin tattara haraji a Nijeriya wajen samun ƙarin kuɗaɗen shiga da bunƙasa zuba jari a ciki da wajen Nijeriya.
No comments