Rikicin da ya barke tsakanin gungun ’yan bindiga da ke gaba da juna ya haifar da ƙazamin harin ramuwar gayya da ya yi sanadin mutuwar mutane...
Rikicin da ya barke tsakanin gungun ’yan bindiga da ke gaba da juna ya haifar da ƙazamin harin ramuwar gayya da ya yi sanadin mutuwar mutane aƙalla goma a kauyen Tofa da ke gundumar Magami a ƙaramar hukumar Gusau a jihar Zamfara.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa rikicin ya fara ne a ranar 22 ga watan Yuni inda wani ɗan bindiga mai suna Uban Gora daga yammacin Tofa ya tare wata mota ƙirar Golf da ta taso daga garin Dansadau tare da yi wa fasinjojin motar fashi.
Wannan lamari dai ya janyo martanin ramuwar gayya daga wani ɗan bindiga da ke zaune a gabashin ƙauyen, inda rahotanni suka ce sun yi arangama tare da harbe Uban Gora har lahira a kan fashin da suka yi ba tare da izini ba.
A cewar Zagazola Makama, kisan ya haifar da tashin hankali a sansanin Uban Gora. A wani mataki na ramuwar gayya, shugaban ‘yan ƙungiyarsa ya tara wasu gungun ‘yan bindiga wazanda suka kai farmaki ƙauyen Tofa a washegarin ranar 23 ga watan Yuni, inda suka buɗe wuta ga mazauna garin. Harin ya yi sanadiyar mutuwar mutanen ƙauyen goma, yayin da wasu da dama suka samu raunuka.
An yi jana’izar waɗanda abin ya shafa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada, amma fargaba da tashin hankali na ci gaba da mamaye al’ummar da abin ya shafa.
Lamarin dai ya nuna yadda rikicin cikin gida ke ƙara ta'azzara a tsakanin ƙungiyoyin 'yan bindiga a Zamfara, inda abin kan ƙare kan fararen hula.
No comments