Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Bayar Da Gudumawa Don Haɗa Kan Hausawa A Ƙasashen Duniya -Tauraruwar Hausa

  Daga Ibrahim Muhammad, Kano Sakamakon kyakkyawar  shaida ta irin gudumuwa  da al'umma suka shaidi Hajiya Samira Bala Usman na bayarwa ...

 
Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Sakamakon kyakkyawar  shaida ta irin gudumuwa  da al'umma suka shaidi Hajiya Samira Bala Usman na bayarwa ga ci gaban al'umma, Gidauniyar  Hausa da  haɗin kan Hausawan Duniya ta tabbatar  mata da  matsayin  'Tauraruwar Hausa da ci gaban Hausawan Duniya' a  yayin wani taro da aka gudanar na Gidauniyar a  jihar Kano.

Da take zantawa da 'yan jarida  bayan karbar shaidar na tabbatar mata da matsayinta na  tauraruwar Hausa da haɗin kan Hausa, Hajiya Samira  Bala Usman ta bayyana mutuƙar murna da farin cikinta game da wannan shaida da aka ba ta na zama  daga cikin shugabanni a Gidauniyar Hausa da Hausawan Duniya "charity.

Ta ce  Gidauniyar ta Hausa da haɗin kan Hausa  tana da himma, ƙwazo da kishi wajen sama wa Hausawan Duniya haɗin kai da  ci gaba a tsarin tafiyar da rayuwar su a duk inda suke.

Ta  ƙara da cewa ta yi mutuƙar  gamsuwa da irin tsare -tsare da Gidauniyar take yi masu ɗimbin  ma'ana wajen tallafa wa gina ci gaban al'umma, musamman ƙoƙarin da take yi wajen hana barace-barace da tallafa wa marayu da kuma  haɗa kan al'ummar Hausawa a  duk inda suka samu kansu a duniya.

Ambasada Hajiya  Samira  Bala  Usman Tauraruwar ta Hausa da Hausawan Duniya.ta  ƙara da nuni da cewa dama ita wannan  Gidauniyar ta Hausa da haɗin kan Hausawa ta Duniya tana da jajicewa wajen ta ga ci gaban al'ummar Hausawa  suma da  suka zama daga mambobinta    za su bada irin tasu  gudunmawa  sosai domin cigaba  ganin ana samun nasarar  hada kan al'ummar Hausawa  a ko'ina a kowace kasa a  fadin Duniya .

Ambasada Hajiya Samira Bala Usman Tauraruwar Hausa da haɗin Kan Hausawan Duniya ta gode wa dukkan waɗanda suka zo don taya ta murna a wannan matsayi da kuma yin kira ga dukkan 'yan ƙungiyar su ci gaba da bada misali  na kyakkyawan haɗin kai a tsakaninsu don gina ci gaban Gidauniyar.
 

No comments