Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Hukumar Tace Fina-finai Ta Jihar Kano Ta Haramta Rubuce-rubuce Ko Liƙa Hotuna A A-daidata Sahu

Daga Ibrahim Muhammad A wani yunƙuri na tabbatar da ɗa'a tare da bin ƙa’idojin doka, Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ƙarƙashin jag...


Daga Ibrahim Muhammad

A wani yunƙuri na tabbatar da ɗa'a tare da bin ƙa’idojin doka, Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba El-mustapha ta sanar da haramta liƙa duk wani nau'in hoto ko kalmomi marasa ma’ana a jikin baburan A-daidaita Sahu a duk faɗin Jihar Kano.

A cewar Jami’in yaɗa labaran Hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya bayyana cewa Shugaban hukumar, Abba El-Mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan samun ƙorafe-ƙorafen al'ummar jihar Kano dangane da yadda masu baburan adai-daita sahu ke nuna hotuna marasa ma’ana ko rubuce-rubuce, inda suke yawo a tituna ba tare da jin kunya ba.

Abba El-mustapha ya ce dokar da ta kafa hukumar ce ta ba ta cikakken iko na sanya ido tare da hukunta masu irin wannan laifi.

Cikin wani salo na tabbatar da bin wannan umarni, Abba El-mustapha ya jagoranci wata tawaga ta musamman domin kai ziyara manyan titunan Kano, wanda suka hadlɗa da Maiduguri Road, Zariya Road, da Sani Marshal Road don a wayar da kan al’umma, musamman masu tuƙa baburan adai-daita sahu kan sabuwar dokar, inda ya nanata cewa hukumar ba za ta sassauta ba wajen hukunta duk wani da aka samu da karya dokokin Hukumar ba komai matsayin sa.

Ya ƙara da cewa, bisa dokar hukumar, duk wani aiki na adabi ko na fasaha dole ne a turo shi gaban ta don tantancewa kafin a fitar da shi ga jama’a. Don haka ana buƙatar al'umma su bada cikakken goyan baya da Kuma haɗin kai domin ci gaban Jihar Kano.

A baya- bayan nan dai idan ba a manta ba, Hukumar ta fita irin wannan aiki na gwaji domin wayar da kan al'umma musamman matuƙa baburan adai-daita sahu, inda ta Sami sama da babura 20  tare da yi musu gargaɗi kafin sabuwar dokarta ta fara aiki.
 

No comments