Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Gwamnatin Tarayya Ta Yi Ta'aziyyar Mutanen Da Suka Rasu A Ambaliyar Garin Mokwa

Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhini bisa ambaliyar da ta auka wa garin Mokwa a Jihar Neja, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare d...


Gwamnatin Tarayya ta bayyana alhini bisa ambaliyar da ta auka wa garin Mokwa a Jihar Neja, wadda ta yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da raba É—aruruwan jama'a da muhallan su.

A wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma'a, Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana da cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya samu cikakken bayani kan halin da ake ciki kan wannan ibtila'in, kuma ya umurci dukkan hukumomin agaji da na tsaro da su ƙara zage dantse wajen gudanar da ayyukan ceto da agaji.

Ya ce: “Tunani da addu’o’in mu suna tare da iyalan da suka rasa 'yan'uwan su da kuma duk waÉ—anda ambaliyar ta shafa.”

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) tare da haɗin gwiwar Sojojin Nijeriya da Gwamnatin Jihar Neja suna aiki ba dare ba rana wajen kai ɗauki ga waɗanda abin ya shafa.

Gwamnatin Tarayya ta yaba da jarunta da sadaukarwar jami’an farko da masu aikin sa kai da ke ci gaba da sanya rayuwar su cikin haÉ—ari don ceton wasu.

Hukumomi na roÆ™on mazauna yankunan da ambaliya ta shafa da su bi umarnin kwashe jama’a daga yankunan da ke cikin haÉ—ari tare da haÉ—a kai da jami’an agaji don tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa.

A cikin sanarwar, Gwamnatin Tarayya ta miÆ™a saÆ™on ta’aziyya ga iyalan waÉ—anda suka rasu, tare da jaddada cewa al'ummar Æ™asar nan suna tare da su a wannan lokaci na jimami, kuma ba za a yi Æ™asa a gwiwa wajen tallafa masu ba.
 

No comments