Daga Ibrahim Muhammad, Kano An bayyana zuwan Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf kan mulki a cikin ɗan lokaci, ya ɗauki matakai n...
Daga Ibrahim Muhammad, Kano
An bayyana zuwan Gwamnan jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf kan mulki a cikin ɗan lokaci, ya ɗauki matakai na kyautata tsarin biyan 'yan fansho haƙƙoƙin su akan lokaci ba tare da jinkiri ko yanke musu wani kaso daga ciki ba.
Mamba na dindindin na ɗaya a hukumar amintattu ta fansho na Jihar Kano, Alhaji Hassan Muhammad Aminu ne ya bayyana hakan lokacin da yake zantawa da manema labarai a madadin shugaban hukumar Fansho ta Jihar Kano, Alhaji Habu Ibrahim Fagge game da cika shekara ɗaya na Gwamnatin Abba Kabir.
Ya para da cewa, Gwamnan ya zo ya amince aka fitar da Naira Biliyan shida don biya kuɗin garatuti na waɗanda su ka yi ritaya, wanda Gwamnatin Ganduje ta shafe shekaru Takwas ba ta biya ba.
Alhaji Hasan ya ka tabbatar da cewe yanzu ma Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sake amincewa da a fitar da Naira Biliyan Biyar da za a sake biyan garatutin a karo na biyu na waɗanda su ka yi ritaya.
Daga nan ya yi nuni da cewa duk da irin wahala da Gwamna Abba Kabir ya sha a wajen 'yan hamayya, da su ka yi yunkuri na Ƙwace wa al'ummar Kano halastaccen zaɓe da suka yi masa, Àllah cikin ikon sa ya tsare shi ya kunyata su ya tabbatar masa da nasara a kotun ƙoli.
Alhaji Hassan Muhammad Aminu ya oara da cewa a matsayin su na muƙarraban wannan Gwamnati suna godiya ga Allah, inda a cikin wannan shekara ɗaya an sami zaman lafiya da inganta kula da tsaro a jihar Kano.
Ya ce dama a fannin bunƙasa ilmi shi ne babban manufar a tafiyar Kwankwasiyya da jam'iyyar NNP, ya zo an ci gaba da tura ɗalibai ƙasashen waje karatu, an gyara makarantu da biya wa ɗalibai kuɗin jarabawa da na makaranta a matakai daban-daba.
Hassan Muhammad Aminu ya ce a ɓangaren lafiya kuwa, an gyara Asibitoci da dama ciki har da ɓangaren gaggawa na Asibitin ƙwararru na Murtala, da dawo da Asibitin Asiya Bayero da a Gwamnatin baya aka rufe.
Sannan kuma ana yin hanyoyi a cikin Birni da karkara ga kuma aikin katafaren gadojin sama yanzu anayi a Dan'agundi da sha tale-talen Tal'udu.
Saboda haka sai Alhaji Hassan Muhammad Aminu ya yi kira ga al'umar jihar Kano su ci gaba da baiwa Gwamna Abba Kabir Yusuf da mataimakinsa Kwamared Aminu Abdussalam cikakken goyon baya da haɗin kai domin ci gaba da inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali da bijiro da ayyuka da za su ci gaba da bunƙasa ci gaban Jihar Kano da al'ummar ta.
No comments