Daga Musa Muhammad Ranar Asabar da ta gabata ne makarantar koyar da harkokin kiwon lafiya ta 'Al'amin School of Health Technology...
Daga Musa Muhammad
Ranar Asabar da ta gabata ne makarantar koyar da harkokin kiwon lafiya ta 'Al'amin School of Health Technology' da ke kan titin bypass, Unguwar Mu'azu Kaduna ta gudanar bikin rantsar da sabbin ɗaliban ta na kakar karatu ta bana.
Taron, wanda ya gudana a harabar makarantar, ya samu halartar iyaye, ɗalibai, 'yan uwa da abokan arziki, inda bayan gabatar da jawabai, sai Magatakardar makarantar ya rantsar da sabbin ɗaliban, tare da gabatar da su ga shugaban makarantar.
Cikin jawabin da ya gabatar, Shugaban taron, Farfesa Yusuf Nadabo ya jawo hankalin sabbin ɗaliban da su mayar da hankali ga abubuwan da za a koya masu, musamman bisa la'akari da babban aikin da ke gaban su na kula da lafiyar jama'a.
Daga nan ya bayyana cewa ya san yanayin yadda ake koyar da karatu a wannan kwaleji. Inda ya bayar da tarihin yadda ya taɓa karo da wani tsohon ɗalibin makaranta, wanda ya kwada shi a hanyar kwamfutar gwaje-gwaje, kuma ya yi yadda ya dace.
Saboda haka sai ya jawo hankalin su, su mayar da hankali ta yadda duk inda suka shiga bayan sun kammala karatun su, za su fitar da kwalejin kunya.
Da ya ke zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala wannan taron, shugaban kwalejin, Malam Umaru Sambo Kusallo ya bayyana cewa "muna farin ciki da wannan rana, inda muka tabbatar wa yara cewa yau sun zama cikakkun ɗaliban wannan malaranta."
Ya ci gaba da cewa, sun tabbatar wa sabbin ɗaliban cewa ba wai karatu kawai ake koyarwa a wannan makaranta ba, suna koyar da hanyoyin dogaro da kai, "domin shi ilimin kiwon lafiya, bayan ka kammala, za ka iya zama mai dogaro da kan ka," ya ce.
Daga nan Malam Kusallo ya baiwa sabbin ɗaliban shawarar cewa su dage su mayar da hankali kan abin da suka zo koyo, domin su a wannan makaranta ba son wasa, suna da tsanani game da jajircewar ɗalibai.
Da ya ke ƙarin haske game da abubuwan da ake koyarwa a wannan makaranta kuwa, shugaban ya bayyana cewa, "muna koyar da kwasa-kwasai bakwai a wannan makaranta, waɗanda suka haɗa da masu kula da lafiya gaba ɗaya, wato community Health.
Sauran sun haɗa da masu koyon bayar da magani, kwaje-gwajen cututtuka, masu bayar da kati, sannan muna koyar da masu duba gari, akwai kuma masu koyon harkar haƙori da kuma masu koyon ɗaukar hoton sassan jiki."
Wannan makaranta dai ta yi fice wajen yaye ɗaliban da suka ƙware a hanyoyin kiwon lafiya daban-daban a duk shekara, bayan sun kammala laratu tare da gudanar kwaji a wasu asibitoci na ɗan wani Lokaci kafin a yaye su.
No comments