Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

El-rufa'i Ya Kwashe Naira Biliyan 423, Inda Ya Bar Jihar Kaduna Da Tulin Bashi -Majalisar Dokoki

Daga Musa Muhammad  Kwamitin da Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta kafa domin binciken yadda Tsohon Gwamnan jihar, Nasiru El-rufai ya gudanar...

Daga Musa Muhammad 

Kwamitin da Majalisar Dokokin jihar Kaduna ta kafa domin binciken yadda Tsohon Gwamnan jihar, Nasiru El-rufai ya gudanar da harkokin kuɗin jihar, musamman ciwo bashi da aiwatar da su, ya miƙa rahoton sa. 

A Lokacin miƙa rahoton a wani zaman Majalisar da ya gudana a Larabar nan, Shugaban kwamitin, Hon. Henry Zacharia ya bayyana sun gano cewa yawancin basukan da gwamnatin El-rufa'i ta ciyo, ba a yi amfani da su don abin da aka ciyo su ba, sannan a wasu wurare ma, ba a bi ƙa'ida wajen ciyo basukan ba. 

Shi kuwa da ya ke karɓar rahoton, Shugaban Majalisar Dokokin jihar, Hon. Yusuf Liman cewa ya yi gwamnatin El-rufa'i ta sace kuɗi kimanin Naira Biliyan 423, tare da barin jihar da ɗimbin basuka. 

Saboda haka sai wannan kwamiti ya bayar da shawarar cewa Hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa, da jami'an tsaro su gurfanar sa Tsohon Gwamna El-rufa'i da wasu muƙarraban sa da aka samu da laifi, don su fuskanci tuhuma game da yadda suka bayar da kwangiloli ba tare da bin ƙa'idoji ba, karkatar da dukiyar jama'a, sata da kuma jefa jihar Kaduna cikin ɗimbin basuka. 

Haka kuma kwamitin ya bayar da shawarar dakatar da Kwamishinan kuɗi na jihar, Shizer Badda, wanda kuma shi ne ya yi wa El-rufa'i Kwamishinan kuɗi. Haka kuma a dakatar da shugaban Hukumar ilimi bai-ɗaya UBE na jihar. 

Ya kuma bayar da shawarar Hukumar tsaro da na yaƙi da rashawa, su binciki wasu da suka riƙe muhimman muƙamai a gwamnatin da ta gabata ta El-rufa'i. 

In dai ba a manta, wannan kafa ta Matattarar Labarai ta kawo maku labarin cewa Majalisar Dokokin jihar ta kafa wannan kwamiti domin ya binciki yadda gwamnatin El-rufa'in ta gudanar ayyukan ta daga shekarar 2015 zuwa 2023.

No comments