Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

SAYAR DA KADARORIN KASA: Matasan APC Sun Zargi Atiku Da El-rufai Da Jefa Al'umma Mawuyacin Hali

 Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ƙungiyar Matasan Arewa da ke da alaƙa da jam’iyyar APC, ta bayyana cewa ƙoƙarin da tsohon mataimakin shugaban ƙ...


 Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ƙungiyar Matasan Arewa da ke da alaƙa da jam’iyyar APC, ta bayyana cewa ƙoƙarin da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ke yi na yi wa gwamnatin shugaba Bola Tinubu zagon ƙasa zai ci tura.

Kodinetan ƙungiyar na ƙasa, Mujahid Zaitawa, ya yi zargin cewa abubuwan da Atiku da El-Rufai suka yi a baya, musamman rawar da suka taka wajen sayar da kadarorin ƙasa a zamanin gwamnatin Obasanjo, ya taimaka wajen taɓarɓarewar tattalin arziƙin Nijeriya a halin yanzu.

Zaitawa ya yi tambaya kan inda kuɗaɗen da ake samu daga waɗannan sayar da kadarorin da suka jagoranta suke, musamman irin na su jiragen sama, NEPA, layin dogo, da kuma gidaje na tarayya da sauran abubuwa da dama .

Ya kuma jaddada cewa ‘yan Najeriya ba za su manta da yadda Atiku da El-Rufai suka gudanar da sayar da kadarorinsun  da  suke neman amsar jin inda aka ajiye kuɗaɗen.

Ƙungiyar ta yi Allah-wadai da yunƙurin Atiku da El-Rufai na komawa kan karagar mulki, inda ta bayyana su a matsayin shugabanni da ba su amfanawa mutane komai ba in ban da sanya su cikin uƙuba.

Zaitawa ya ƙara da cewa ‘yan Nijeriya za su yi watsi da duk wata buƙatarsau ta neman  shugabanci, sannan da shigar da ƙara a gaban hukumomin yaƙi da almundahana da cin hanci da rashawa kan zargin karkatar da kuɗaɗen na sayar da kadarorin ƙasa.

Ƙungiyar ta bai wa Atiku da El-Rufa'i wa'adin  mako biyu, idan ba su  amsa tuhumar da ake musu ba a kan yadda suka sami dama ta tsarin dimakraɗiyya daga yankin Arewa suka jefa ƙasar nan cikin matsalar da yanzu take biyar al'umma ba, za su rubuta wa EFCC da ICPC ƙorafi da zai bankaɗo yadda suke da hannu a kan wannan kadarorin ƙasa da shi ne silar jefa ƙasar nan a mawuyacin hali da   ake ciki yanzu.
 

No comments