Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

BAYAN KAMMALA HUTUN SA: Yau Shugaba Tinubu Zai Dawo Gida

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa yau Litini ne ake sa ran dawowar Shugaba Bola Tinubu gida daga Faransa, bayan kammala hutun da ya yi a c...

Fadar shugaban ƙasa ta bayyana cewa yau Litini ne ake sa ran dawowar Shugaba Bola Tinubu gida daga Faransa, bayan kammala hutun da ya yi a can.

 Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga ya sanar da haka a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, inda ya ce Shugaba Bola Tinubu zai hau jirgi ya dawo gida yau Litinin.

Sanarwar ta ce, "Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai dawo gida yau Litinin, 21 ga Afrilu, wacce ta yi daidai da ranar Easter.

Wannan sanarwa ta Kakakin shugaban ƙasan, ta kawo ƙarshen cece-kucen da ke yawa, na cewa shugaban ya je Faransa ya yi zaman sa.
 

No comments