Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Malam Abdulaziz Abdulaziz Ya Ɗauki Nauyin Horar Da Matasa 50 Ilimin Fasahar Zamani

  A ƙoƙarinsa na tallafa wa mata da matasa domin su samu wayewar zamani da abubuwan dogaro da kai, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa, B...

 
A ƙoƙarinsa na tallafa wa mata da matasa domin su samu wayewar zamani da abubuwan dogaro da kai, mataimaki na musamman ga shugaban ƙasa, Bola Ahmad Tinubu kan harkokin sadarwa, Malam Abdulaziz Abdulaziz ya ɗauki nauyin horar da matasa 50 ilimin fasahar sadarwar zamani.
 
Horon wanda ya gudana tare da haɗin-gwiwar (Shabala Productions Computer Academy) da ke Kano, an koya wa matasan hanyoyi da dabarun cin gajiyar damarmakin da ke tattare da fasahar zamani, da yadda ake ƙirƙirar abubuwa na fasahar zamani da sauran fannoni masu alaƙa.


Bayan kammala horon, an gudanar da bikin yaye matasan a wannan rana tare da raba na’ura mai ƙwaƙwalwa ga waɗanda suka fi nuna hazaƙa.
 


No comments