Daga Zubairu Lawal, Jos Kungiyar da ke fafutukar gyara ɗabi'u da haɗin kan 'yan Nijeriya, Advocacy for Intergrety And Rule of Law In...
Daga Zubairu Lawal, Jos
Kungiyar da ke fafutukar gyara ɗabi'u da haɗin kan 'yan Nijeriya, Advocacy for Intergrety And Rule of Law Initiative (AIRLIN) ta buɗe ofishin ta na biyar, wanda a wannan karon aka buɗe na jihar Filato a garin Jos.
Ƙungiya mai zaman kanta da ke ƙarfafa wayar da kan jama'a da bin doka a Nijeriya, ta Ƙaddamar da ofishin ta a Jos, wanda ke nuna mataki mai muhimmanci a faɗaɗa ayyukan ta a yankin Arewa.
A yayin bikin ƙaddamarwar, Shugaban Ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Ibrahim Mohammed Gamawa, ya gabatar da jawabi mai muhimmanci, inda ya jaddada aniyar ƙungiyar na ilmantar da 'yan Najeriya game da haƙƙoƙinsu na ɗan ƙasa da nauyin da ke kansu.
Gamawa ya bayyana cewa, Airlin na da burin cike giɓin da ke tsakanin 'yan ƙasa da ƙa'idodin bin doka ta hanyar ƙarfafa al'umma su fahimci haƙƙoƙinsu da abin da ake tsammani daga gare su a matsayin 'yan ƙasa.
"Muna da burin ƙarfafa hulɗa tsakanin 'yan Najeriya, ƙarfafa girmama bin doka, da tabbatar da cewa 'yan ƙasa sun san haƙƙoƙinsu da nauyin da ke kansu na ɗan ƙasa, kamar yin zaɓe don zaɓar shugabanni masu gaskiya da ƙwarewa, ba bisa son zuciya ba," in ji Gamawa.
Ya ƙara da cewa, fahimta da amfani da haƙƙin zaɓe, musamman a lokacin zaɓe, dole ne su tafi tare da bin doka da cikakken sanin nauyin da ke kan ɗan ƙasa.
A matsayin wani ɓangare na aikin ta, Airlin na niyyar faɗaɗa ayyukanta zuwa jihohi 19 a Arewacin Nijeriya, inda Jos ta zama jiha ta 5 da aka kaddamar da ofishi, baya ga Bauchi, Nasarawa Neja, Katsina da Filato.
Bikin ya kuma haɗa babban kodineta mai kula da jiha da ƙananan hukumomi 18 waɗanda za su taimaka wajen haɓaka ƙoƙarin ƙungiyar na wayar da kan jama'a a matakin hada kai da zaman lafiya.
Haka zalika, aikin ƙungiyar ne wayar da kan matasa su guji ta'ammali da miyagun kwayoyi, sannan fadakar da direbobi a guji tuƙin ganganci da mummunar lodi.
Haka zalika, ƙungiyar tana wayar da kan ’yan kasa su gujewa siyasar kuɗi domin shi ke gurɓa shugabanci.
Ya ce; kungiyar ta malliki na'urorin yin katin shidar ɗan kasa, inda take yi wa mutane kyauta har gidajensu.
Tunda farko a taron an jajantawa al'umman da bala'in harin ’yan bindiga ya shafa a jihar Filato a ranar Littinin.
Membobin ƙungiyar da aka ba su takardan kama aiki sun sha alwashin tabbatar da zaman lafiya a jihar Filato.
Ƙungiyar tace tana da kwarin guiwar samar da mutanen sama da miyilyon 7 a faɗin Nijeriya.
A yanzu haka tana kokarin buɗe ofishoshinta 19 a Arewacin Nijeriya
No comments