Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

'Rasuwar Galadiman Kano Babban Rashi Ne'

Daga Ibrahim Muhammad, Kano Ɗan kasuwa, kuma shugaban rukunin kamfanonin  Hamir, Alhaji Hamisu Rabiu Jingau ya nuna mutuƙar alhininsa bisa r...

Daga Ibrahim Muhammad, Kano

Ɗan kasuwa, kuma shugaban rukunin kamfanonin  Hamir, Alhaji Hamisu Rabiu Jingau ya nuna mutuƙar alhininsa bisa rasuwar Galadiman Kano, babban ɗan majalisar masarautar Kano, Alhaji Abbas Sanusi da ya rasu ranar talata, inda ya ce wannan babban rashi ne ga al'ummar Kano.

Ya yi nuni da cewa an yi rashi na Uba, jagora wanda kullum yake ƙoƙarin haɗa kan al'umma  da  nusar da muhimmancin zaman lafiya garesu.

Alhaji Hamisu Rabiu, wanda ya bayyana hakan a lokacin da yake zantawa da 'yan jarida a yayin da ya kai ziyarar ta'aziyya gidan marigayin, ya ce a matsayinsu na masu tasowa za su ci gaba da koyi da halaye managarta na irin waɗannan magabata da suka bayar da gummuwa wajen haɗin kan al'umma da mutuntawa.

Shi ma a tasa yayin ta'aziyyar, shugaban kamfanin taki na Alyuma, Alhaji Ali Mai taki  ya ce rashin Galadiman Kano Alhaji Abbas rashi ne babba mai wahalar cikewa idan aka yi la'akari da irin gudummuwar da ya bayar ga ci gaban al'umma.

Alhaji Ali Mai taki ya ce za a ci gaba da tuna marigayi Galadima da irin gudummuwa da ya bayar, su kuma al'umma da iyalansa za su yi  haƙuri da wannan rashi da aka yi.

 

No comments