Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da cewa za a samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga sakamakon ci gaban da aka samu a fannin tsaro a faɗin...
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya tabbatar da cewa za a samu ƙaruwar kuɗaɗen shiga sakamakon ci gaban da aka samu a fannin tsaro a faɗin jihar.
A ranar Larabar da ta gabata, gwamnan ya zagaya wurare da masana'antar haƙar ma'adinai a ƙananan hukumomin Anka da Maru.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa ziyarar na da nufin gano ɗimbin albarkatun jihar Zamfara da kuma samar da ƙarin hanyoyin samun kuɗaɗen shiga.
“A yau ne Gwamna Dauda Lawal ya fara rangaɗin wuraren haƙar ma’adanai da masana’antu, inda ya fara ziyarar aiki a wani kamfani mai zaman kansa na Comet Star Industry da ke Ƙaramar Hukumar Anka.
“Ma’aikatar, mallakin Prince James Uduji OON, tana sarrafa kusan tan 1,000 a kullum. Tana da cikakkiyar kayan aiki da sabbin fasahohin haƙar ma’adinai don tabbatar da gudanar da ayyuka masu inganci.
“Lokacin da je masana’antar, Gwamna Lawal ya zagaya wurare da dama, inda ya fara tun daga magudanar ruwa da zuwa duka sassan injina da kayan aiki.
"Gwamna Lawal ya kuma ziyarci wurare daban-daban a cikin masana'antar, ciki har da gidan wutar lantarki da ke samar da wutar lantarki ga ɗaukacin kamfanin, da ɗakin gwaje-gwajen da ake sarrafa kayayyakin."
A jawabinsa jim kaɗan bayan kammala rangaɗin, Gwamna Lawal ya bayyana gamsuwarsa da ƙa’idojin masana’antar, inda ya bayyana cewa irin jarin da gwamnatin jihar ke nema kenan.
“Na ji daɗi a yau domin wannan ya nuna ƙarara cewa an samu nasara a fannin tsaro a jihar Zamfara, ina godiya ga sojoji da duk masu ruwa da tsaki da suke aiki tuƙuru domin samar da zaman lafiya.
“Bugu da ƙari, ana ci gaba da tattaunawa tsakanin Gwamnatin Tarayya, Gwamnatin Jiha, kamfanoni masu zaman kansu, da sauran al’umma don fahimtar kadarorinmu da kuma gano alfanun su, wannan jiha tana da albarkar ma’adanai masu inganci, idan har za mu iya gano amfani su, ina tabbatar muku cewa za mu inganta kuɗaɗen shiga da kuma bunƙasa jihar Zamfara cikin sauri.”
A Ƙaramar Hukumar Maru, Gwamna Dauda Lawal ya yi wa masu haƙar ma'adan alƙawarin cikakken goyon bayan gwamnati, matuƙar suna aiki yadda doka da ƙayyade
Gwamnan ya yi alƙawarin samar wa da ma'aikatan muhimman kayan aiki don kauce wa gurɓatar muhalli.
Ya ce, “Muna haɗin gwiwa da gwamnatin yarayya, kuma suna ɗaukar muhimman matakai don aiwatar da abubuwan da suka wajaba. Zan turo Kwamishinan muhalli ya zauna da kuma, ta yadda kowa zai iya yin rajista. Ta hanyar rajista ne kawai za mu iya taskace sahihan bayanai.
“Gwamnatin jiha za ta samar maku da tallafin da ya wajaba, wanda zai haɗa da samo maku mataƙaicin izinin aikin haƙar ma'adanan daga gwamnatin tarayya, amma dole sai kun kafa ƙungiyoyin taimakon kai da kai.”
No comments