Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Ku Yi Gaggawar Magance Matsalar Tsaro - Tinubu Ya Umarci Hukumomin Tsaron Nijeriya

Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaron ƙasar su gaggauta kawo ƙarshen matsalar tsaro da take ƙara ƙamari a jihohin Borno da Fi...


Shugaban Ƙasa Bola Tinubu ya umarci hukumomin tsaron ƙasar su gaggauta kawo ƙarshen matsalar tsaro da take ƙara ƙamari a jihohin Borno da Filato da Binuwai da kuma Kwara.

A wata sanarwa da ɗaya daga cikin masu magana da yawun shugaban Nijeriyan, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya bayyana damuwa kan kisan ’yan Nijeriya da basu ji ba, ba su gani ba a sassan ƙasar.

Wannan na zuwa ne bayan shugaba Tinubu ya gana da shugabannin tsaron ƙasar a fadarsa da ke Abuja, inda suka yi nazari a kan yanayin tsaro a Nijeriya.

Shugaban ƙasan wanda ya shafe fiye da sa'oi biyu yana ganawa da shugabannin hukumomin tsaron Nijeriya, ya ce dole ne su kawo ƙarshen kisan mutane a ƙasar.

Sanawar ta ambato Shugaba Tinubu na shaida wa hafsoshin tsaron cewa daga ɓangarensa fa "tura ta riga ta kai bango, domin haka wajibi ne su tashi tsaye domin samar da mafita game da halin da Nijeriya ke ciki a kan tsaro".

Dama dai shugaban ƙasar ya umarci shugabannin tsaron su yi aiki tare da hukumomin jihohin da ke da matsalolin tsaro a Nijeriya domin cimma matsaya a kan matakin bai ɗaya da ya fi dacewa a ɗauka a kai tun daga tsuhe.

A kan haka ne kuma shugabannin hukumomin tsaron suka sake komawa domin yi wa shugaba Tinubu bayanin abubuwan da suka gano kawo yanzu.

Mai bai wa shugaban Nijeriya shawara a kan tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce a yayin taron na ranar Laraba, an yi kyakkyawan Nazari game da matsalolin tsaron ƙasar da ma matakan da ya kamata a ɗauka a kai.

Ya ce: "A wannan karon mun zauna da shugaban kasa kuma mun shafe sa'oi muna yi masa bayani dalla-dalla. Yayin da kuma muka amsa sabbin umarnin a kan ayyukan tabbatar da tsaro.

"Shugaban ƙasar na aiki tuƙuru domin ganin ƴan Nijeriya suna rayuwa cikin kwanciyar hankali da tsaro. Ba za mu gajiya ba har sai mun cimma burin mu na samar da tsaro ga jama'a.''

A game da dawowar hare-haren Boko Haram a jihar Borno kuwa, Malam Nuhu Ribadu ya ce "Maƙiyan namu ba su miƙa wuya cikin sauƙi. Kuma suna mafani da dabarun kai hare-hare ne domin nuna cewa har yanzu suna nan da ƙarfin su, da kuma sanya tsaro a zukatan mutane.''

No comments