Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta sake ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu. Ƙaramin Ministan ma...
Gwamnatin Tarayya ta sanar da cewa za ta sake ƙaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu.
Ƙaramin Ministan ma'aikatar jin ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami’an gwamnati a Abuja.
Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara ta biyu akan karagar mulki.
Ya ce shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin ƙasar baki ɗaya.
''Shirin na nufin amfanar yara miliyan 10 kuma zai iya ƙara yawan yaran da ke shiga makarantu da kashi 20 cikin 100 sannan kuma ya bunƙasa hazaƙar yara a ɓangaren karatu da kashi 15 cikin 100 ,” inji shi.
No comments