Daga Ibrahim Muhammad, Kano Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yana daga cikin Gwmnonin da aka karrama a yayin bikin karramawar jari...
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf yana daga cikin Gwmnonin da aka karrama a yayin bikin karramawar jaridar Leadership karo na 17 da aka gudanar a ɗakin taro na Banquet da ke fadar shugaban ƙasa, Abuja.
A taron an karrama fitattun ‘yan Nijeriya da suka yi rawar gani a fannoni daban-daban, ciki har da Alhaji Aliko Dangote, wanda ya zama gwarzon shekara ta 2024, da Gwamnan Jihar Jigawa, wanda kuma ya samu kyautar Gwarzon Gwamna.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, an bayyana wannan karramawar a matsayin tabbatar da sauye-sauyen da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a fannin ilimi, wanda ya dawo da tasirin sa a jihar Kano bayan shekaru da dama da aka yi watsi da shi.
An yaba wa Gwamna Yusuf musamman kan ware kashi 31% na kasafin kuɗin jihar ga ilimi, wanda ya zarce na UNESCO, da kuma kafa dokar ta-ɓaci a fannin.
Shirye-shiryen gwamnatinsa sun haɗa da manyan gyare-gyaren makarantu, samar da kayayyakin koyo, ɗaukar Malamai, da ƙaddamar da wani cikakken tsarin farfaɗo da ilimi.
Da yake jawabi bayan karɓar lambar yabon, Gwamna Yusuf ya nuna godiya ga waɗanda suka shirya taron, inda ya bayyana karramawar a matsayin ba zato ba tsammani .
“Ba mu taÉ“a tunanin cewa Æ™oÆ™arinmu zai samu karÉ“uwa irin wannan a Æ™asa ba, ba mu biya kuÉ—i don wannan lambar yabo ba, an gane mu ne kan abin da muka samar a Kano,” in ji Gwamnan.
Daga nan sai Gwmnan ya sadaukar da kyautar ga yara marasa galihu a faÉ—in jihar, tare da jaddada aniyar gwamnatinsa na zurfafa gyare-gyare a fannin ilimi.
Ya kara da cewa "Wannan karramawa ta ƙara ba mu ƙwarin gwiwa don ci gaba da yunƙuri don samar da ilimi mai nagarta. Ina godiya ga mahukuntan jaridar Leadership da kuma kafafen yaɗa labarai saboda ci gaba da goyon bayan da suke bayarwa."
No comments