Aƙalla mutum 40,000 ne za su ci gajiyar shirin Aliko Dangote na tallafin abinci. Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce tall...
Aƙalla mutum 40,000 ne za su ci gajiyar shirin Aliko Dangote na tallafin abinci.
Gwamnan jihar Borno Farfesa Babagana Umara Zulum ya ce tallafin buhunan shinkafa 40,000 masu nauyin kilogiram 10 da gidauniyar Aliko Dangote (ADF) ta bayar ga al’ummar jihar Borno zai taimaka wajen daĆ™ile matsalar tattalin arziki.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a wajen ƙaddamar da shirin bayar da abinci a ranar Laraba a Maiduguri, babban birnin jihar Borno.
Gidauniyar Aliko Dangote ta ƙaddamar da rabon buhunan shinkafa miliyan ɗaya da kuɗin su ya kai Naira biliyan 16 a faɗin ƙananan hukumomi 774 na Nijeriya.
Gwamnan ya samu wakilcin Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Borno (SEMA) Ali Abdullahi Isa.
Ya ce: “A yau an samu wani gagarumin ci gaba ne a Ć™oĆ™arin da muke yi na rage raÉ—aÉ—in da al’ummarmu ke ciki, musamman a wannan wata na Ramadan.
Gwamnan ya ce, tallafin da aka bayar ya shaida yadda gidauniyar ta himmatu wajen tallafa wa marasa galihu da kuma inganta jin daÉ—in jama’a.
"Muna matuƙar godiya ga Alhaji Aliko Dangote da kuma gidauniyar baki ɗaya bisa irin wannan alheri da suka nuna."
Ya buĆ™aci al’ummar jihar Borno da su ci gaba da yi wa jihar da Ć™asa addu’ar zaman lafiya da kwanciyar hankali.
A jawabinsa na farko, wakilin gidauniyar Aliko Dangote, Usman Muhammad, ya ce sun ĆŠauki wannan mataki ne da nufin tallafawa Ć™oĆ™arin gwamnati, inda ya Ć™ara da cewa gidauniyar ta mayar da hankali ne wajen inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.
Muhammad ya ce, an yi niyyar ba da tallafin ne ga talakawa da marasa galihu a jihar.
Wata mata cikin waÉ—anda suka ci gajiyar tallafin, Aisha Modu, mai shekaru 50, ta ce a matsayinta na ‘yar gudun hijira, tallafin shinkafar da ADF ta bayar zai taimaka matuĆ™a wajen rage mata matsalolin tattalin arziki.
Hakazalika, wani wanda ya ci gajiyar shirin mai suna Umaru Aliyu mai shekaru 60, ya ce zai yi amfani da shinkafar ne wajen ciyar da ‘ya’yansa shida, yayin da ya yi addu’ar Allah ya ci gaba da yi wa shugaban gidauniyar Aliko Dangote albarka.

No comments