Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

Za Mu Ɗauki Mataki Mai Gauni Ga Masu Tafsirin Zage-zage Da Raba Kan Musulmi -Shugaban Jama'atu

Ganin cewa sauran 'yan kwanaki kaɗan a soma Azumin watan Ramadan, a bana ma ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam JNI ta shirya taron wayar...

Ganin cewa sauran 'yan kwanaki kaɗan a soma Azumin watan Ramadan, a bana ma ƙungiyar Jama'atu Nasril Islam JNI ta shirya taron wayar da kai da jawo hankali, musamman ga Malamai masu gabatar da tafsiri a masallatai da sauran wurare, kamar dai yadda ta saba duk shekara, don tsawatarwa game da furta kalaman da ka-iya kawo saɓani da rarraba a tsakanin musulmi. 

Taron na bana ya gudana ne ranar Litini da ta gabata a Sakatafiyar ta JNI ta ƙasa da ke Kaduna, wanda kuma ya samu halartar manyan Sarakunan Arewacin ƙasar nan, manyan Malamai da sauran jama'a, a ƙarƙashin jagoranci mai alfarma Sarkin musulmi Alhaji Sa'adu Abubakar.

Cikin jawabin da ya gabatar, Shugaban na Jama'atu Farfesa Khalid Abubakar Aliyu ya yi kakkausar suka ga Malamai masu tafsirin ɓatanci ga juna, waɗanda ya kira da Malaman Soshiyal Mediya, su ba ilimi ba, amma sai neman a san su. 

Ya ce ba za su zura ido suna ganin wasu na fakewa da sunan tafsiri suna rarraba kan musulmi ba. Ya ce, akwai hukunci mai tsanani da za a ɗauka ga duk wanda ya saɓa wannan doka.

"Ba za a bar Malamai su riƙa cin karen su babu babbaka ba. Kowa ya raɗa wa kansa suna 'Shaikh', idan ka tambaye shi, wa ya naɗa masa 'Shaikh', kowa ya naɗa kansa 'Shaikh', ya ɗauki abin magana, kowa sai ya yi maganar da ta girmi kakansa, wacce bai taɓa jin ta ba, Malamai ba su faɗa ba. Kowa yai ta sake maganganu marasa daɗi.

Tun kafin Ramadan, wata ɗaya baya na, kun ga abin da ya faru. Yanzu kuma kowa ya kaffaɓe teburin sa, ya zagi wancan, ya harbi wannan, ya ɓaci wannan. To gaskiya shugabanci ba zai yarda da wannan ba. 

"A wancan lokacin, haka aka yi da Ɗangungu (Malam Usman Ɗangungu), kan a tsayar da shi. Amma dayake akwai shaƙiyyai tattare da shi, suka sa aka tafi kotu, tun daga Majistare, aka je High Court har zuwa Federal High Court. 

"Saboda haka nan gaba dole ne a samu yanayi, ƙarƙashin mai alfarma, tare da gwamnati, dole a sa doka yadda za a rinƙa wa'azi, abubuwan sun wuce inda ake tsammani."

Da ya ke ƙalubalantar masu tafsirin, waɗanda ya kira da na zamani, 'yan Soshiyal Midiya, Farfesa Khalid cewa ya yi, "in mutum ya isa ya shiga Muhtasar mana, in mutum ya isa ya shiga Askari mana. Ya zo ya sa muhtasar, ya zo ya sa Askari, ya ɗauki Mudawwana in ya isa, ya ɗauko Daliya in ya isa. Amma Ƙur'ani ne aka raina, kowa zai zo ya ɗauka ya yi abin da ya ga dama, ba za mu lamunta ba."

Shugaban na Jama'atu ya ce, "Duk wanda ya yi ba-daidai ba, to tsumagiyar horo za ta shafɗe shi, don mu huta da 'yan bani-na-iya, 'yan dole sai ni, 'yan na zo in bayyana kaina, da dai sauran su. 

"Waɗannan su ne muke fata, kuma Allah ya sa mu yi Azumi lafiya. Allah ya sa Malamai su yi tafsiri lafiya."

Haka kuma Farfesa Khalid ya bayyana cewa baya ga masu tafsiri, Limancin masallatai ma ba za su bar shi haka nan kara-zube ba, "Yanzu haka muna da bayanan Malamai, akwai inda aka ce wane zai iya limanci, amma ba zai iya tafsiri ba, wane kuma zai iya tafsiri, amma ba zai iya limanci ba. Dukkan takardun na nan mun tattara," in ji shugaban na Jama'atu. 

 

No comments