Grid

GRID_STYLE

Grid

GRID_STYLE

Hover Effects

TRUE

Pages

Labarai:

latest

A Ƙarshe Dai El-Rufa'i Ya Fice Daga APC, Ya Bayyana Komawar Sa SDP

Bayan dogon lokacin da aka ɗauka ana raɗe-raɗin cewa tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai zai fice daga jam'iyyar su ta APC...


Bayan dogon lokacin da aka ɗauka ana raɗe-raɗin cewa tsohon Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru El-rufai zai fice daga jam'iyyar su ta APC, yanzu dai ta tabbata, ya fice daga jam'iyyar.


Cikin wata sanarwa da ya sa a shafin sa na facebook, Malam Nasiru ya bayyana cewa a yau 10 ga watan Maris na 2025 ya miƙa takarsarsa ta ficewa daga Jam'iyyar APC, wacce ya miƙa a mazaɓar sa a Kaduna. Haka kuma nan take ya ce ya koma jam'iyyar SDP. 


Tsohon Gwamnan ya yi ƙorafin cewa yana daga cikin waɗanda suka kafa APC, amma lokacin da ya ga abubuwa na tafiya ba-daidai ba, ya yi magana a asirce, har ya fito fili ya yi magana don a gyara, amma aka ƙi. 


Don haka ya ga cewa zaman sa a jam'iyyar ba zai kawo wani ci gaba ba, ficewar sa ce ta fi alhairi, don haka ya fice. 


A ƙarshe ya bayyana cewa zai kai gauro ya kai mari don jawo sauran jam'yyun hamayya su shigo SDP don ceto ƙasar nan daga lalacewa

No comments